Dan haya ya yiwa matar mai gida da dan ta duka

Dan haya ya yiwa matar mai gida da dan ta duka

- Wani dan haya, Aliyu Mohammed ya doki matar mai gidan hayar da ya ke zaune

- Mohammed ya gayyaci abokansa biyu ne suka taru suka doki matar mai gidan hayar da dan ta

- Sai dai dan hayar ya musanta cewa ya doki matar mai gidan yayin da ya bayyana a kotu

An gurfanar da wani dan haya mai suna Aliyu Mohammed mai shekaru 27 a kotun Majistare da ke Ikeja a Legas a yau Alhamis, bisa zarginsa da yiwa matar maigidan da dan ta duka.

Mohammed dai dan kasuwa ne kuma yana zaune a unguwar Dopemu da ke Agege a jihar Legas.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Clifford Ogu ya ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Augustan 2018 a gidan da ya ke zaune.

Dan haya ya yiwa matar mai gida da dan ta duka
Dan haya ya yiwa matar mai gida da dan ta duka
Asali: Twitter

Ogu ya ce wanda ake zargi da wasu abokansu biyu ne suka hada baki suka doki matar mai gidan hayar da dansa sai dai sauran mutane biyun sun tsere.

DUBA WANNAN: Tsautsayi ya fada wa Soji biyu a wasan bindiga kuma sun mutu

"Wanda ake zargi ya kawo abokansa inda suka doki matar mai gidan hayar, Mrs Eunice Onatayo da dan sa Mr Akinkum Onatayo.

"Wanda ake zargin ya ji musu rauni a jiki," inji mai shigar da karar.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa idan laifin ya tabbata, sashi na 173 ya tanadi hukuncin zaman gidan yari na shekaru 2 yayin da sashi na 411 ya tanadi zaman gidan yari na shekaru 4 na hadin baki.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan kuma kotu ta bayar da belinsa kan kudi N50,000 tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Alkalin kotun, Mrs J.A Adegun ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 4 ga watan Ocktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel