Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari

Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dare madafan ikon Najeriya, inda ya karbi mulki daga hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sai dai tun bayan darewarsa wannan mukami, abubuwa da dama sun faru a gwamnatinsa.

Daga cikin wadannan lamurra da suka dauki hankulan yan kasa akwai murabus da wasu minitocinsa suka yi, ma’ana wasu ministoci a gwamnatin shugaba Buhari sun ajiye aikinsu, wasu ta dadi wasu kuma ta akasin haka.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya gargadi sabon mataimakinsa kan abinda dayake bukata daga wajensa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jimillan ministoci guda uku ne dake rike da manyan mukamai suka yi murabus tun daga farkon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa yanzu, daga cikinsu kuma akwai.

Amina Mohammed

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Amina Muhammed ne a matsayin ministar muhalli mai wakiltar al’ummar jahar Gombe a majalisar zartarwa, a ranar 11 ga watan Nuwambar 2015.

Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari
Amina
Asali: Depositphotos

Sai dai Hajiya Amina ta yi murabus a ranar 24 ga watan Feburairun shekarar 2017 bayan ta samu cigaba, inda babban sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterez ya zabeta a matsayin mataimakiyar sakatariyar majalisar dinkin duniya, lallai likafa ta yi gaba.

Kayode Fayemi

Tsohon gwamnan jahar Ekiti Kayode Fayemi na daga cikin yan gaban goshin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya nada shi mukamin ministan albarkatun kasa, a ranar 11 ga watan Nuwamban 2015.

Sai dai Fayemi yayi murabus daga gwamnatin shugaba Buhari a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2018 don ya fafata a takarar gwamnan jahar Ekiti karo na biyu, kuma ya samu sa’a ya lashe zaben a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari
Fayemi da Kemi
Asali: UGC

Kemi Adeosun

Kamar dai sauran takwarorinta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Kemi Adeosun ne a matsayin ministar kudi a ranar 11 ga watan Nuwambar 2015, inda ta kwashe fiye da tsawon shekaru uku tana rike da wannan mukamin.

Sai dai Kemi ta fara shiga matsala ne a daidai lokacin da aka bincike tana amfani da shaidar tsallake bautan kasa na bogi, wanda tace wasu data amince musu ne suka yo mata takardar, wanda hakan yasa a ranar 14 ga watan Satumba ta yi murabus daga mukaminta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel