Abinda Babangida (IBB) ya fada min bayan na nemi ya goyi bayan Buhari a 2019 - Orji Kalu

Abinda Babangida (IBB) ya fada min bayan na nemi ya goyi bayan Buhari a 2019 - Orji Kalu

A ranar ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya ziyarci tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) a gidansa dake Minna ta jihar Naija domin neman ya goyi bayan takarar Buhari a zaben shekarar 2019.

Kalu ya bayyana cewar IBB ya fada masa cewar yana kokwanto a kan goyawa Buhari baya domin ya lashe zaben shekarar 2019.

Tsohon gwamnan ya shaidawa manema labarai cewar shugaba Buhari ya cancanci a sake zabensa saboda shine zai iya ceto Najeriya.

A cewar Kalu: "Na zo garin Minna ne domin yiwa Buhari yakin zabe bayan na ga yadda 'yan takarar PDP ke tururuwar zuwa wurin IBB domin neman goyon bayansa.

Abinda Babangida (IBB) ya fada min bayan na nemi ya goyi bayan Buhari a 2019 - Orji Kalu
Orji Kalu yayin da ya ziyarci IBB ranar Talata
Asali: UGC

"Na zo domin mu yi magana da shi ta fuskantar juna da kuma bashi hujjojin da zasu saka shi ya gamsu cewar shugaba Buhari ne dan takarar da ya dace ya goyawa baya.

"Amsar da ya bani ita ce cewar har yanzu yana tunani a kan goyawa Buhari baya. Akwai ragowar lokaci kafin watan Fabrairu da za a gudanar da zaben shugaban kasa kuma zamu cigaba da tattaunawa kafin lokacin; ina da karfin gwuiwar cewar zai goyi bayan Buhari," a kalaman Kalu.

DUBA WANNAN: APC ta canja ranakun gudanar da zabukan fitar da 'yan takara

Kalu ya kwatanta shugaba Buhari da cewar tamkar dan wasan kwallon kafa ne da ya buga wasa na mintuna 45 a zagayen farko kuma yanzu zai koma domin sake buga wasa na wasu mintuna 45 din a zagaye na biyu.

Daga karshe, Kalu ya bukaci 'yan Najeriya da su bawa shugaba Buhari dama domin kammala zagaye biyu na mulkinsa da doka ta amince da shi domin, a cewar sa, hakan mafi alheri ga Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel