Fitattun 'Yan 'Kwallo 5 da suka tashi cikin Talauci kuma suka zamto Hamshakai

Fitattun 'Yan 'Kwallo 5 da suka tashi cikin Talauci kuma suka zamto Hamshakai

A yayin da duniya ta kasance mai yayi kuma juyi-juyi, a yau jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu fitattun 'yan kwallon kafa biyar 'yan asalin nahiyyar Afirka da suka taso cikin tsatso na talauci amma yanzu sun zamto hamshakan attajiarai.

Wadannan mashahuran 'yan kwallo sun sassake duk wani katutu na talauci bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo cikin sa tsatson tun farkon rayuwar su.

Da yake Hausawa kan ce arziki kashi ne kuma tako shi ake, hakika wannan fitattun 'yan kwallo sun tako shi kane-kane a sawayensu inda a halin yanzu suke fantamawa da wadakar rayuwar cikin yalwar arziki.

Legit.ng ta kawo muku jerin wannan fitattun 'yan kwallo tare da hotunansu da ta kalato a shafukansu na sada zumunta da kuma takaitaccen tarihi kan tarin dukiya da Mai Duka ya azurta su da ita.

1. Stephen Apiah

'Dan asalin kasar Ghana da ya fara takawa kasar sa leda a tun yana shekaru 15 a duniya. Ya karade kungiyoyin kwallon kafa kamar su Juventus, Fenerbahce, Udinese da sauransu yayin da a halin yanzu yana daya daga cikin attajiran 'yan kwallon kafa na a tarihin kasar Ghana.

2. Samuel Eto'o

Fitaccen dan kwallon kafan da ya fito daga cikin wani kauyen a garin Doualla na kasar Kamaru, Samuel Eto'o ya taso yana kwana bisa makwaci daya tare da 'yan uwansa 6 inda a halin yanzu yana da tarin dukiya ta kimanin Dalar Amurka miliyan 80.

Eto'o ya taka leda a kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Barcelon da kuma Barcelona.

3. Christian Atsu

Christian Atsu dan asalin kasar Ghana yana da tarin dukiya ta kimanin Dalar Amurka miliyan 12. Ya taka leda a kungiyoyin kwallon kafa na FC Porto, Chelsea da kuma Bournemouth bayan ya taso yana sayar da ruwan leda domin yakar talauci na nemawa 'yan uwansa abin dogaro da kuma lasawa a baka.

4. Yaya Toure

Wannan mashurin dan kwallon kafa ya fito daga kasar Cote d'Ivoire, Yaya Toure, ya samu dukiya mai tarin yawa yayin da ya shafe tsawon rayuwarsa ta sana'ar sa ta kwallon kafa a kasashen Belgium, Ukraine, Greece, France, Spain da kuma Ingila inda yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.

KARANTA KUMA: Adadin kudade da Gwamnatin tarayya ta bai wa kowane Jami'in tsaro yayin Zaben jihar Osun

5. Steven Pienaar

Pienaar, wanda dan asalin kasar Afirka ta Kudu ne, ya tako kashi na arziki yayin da ya fara sana'arsa ta kwallon kafa a kungiyar Ajax inda a halin yanzu yake ci gaba da sharar fage a kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth dake kasar Ingila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel