Gwmnatin Tarayya ta sayar wa da babban bankin CBN hannayen jarinta 12 biliyan dake Kamfanin buga kudi

Gwmnatin Tarayya ta sayar wa da babban bankin CBN hannayen jarinta 12 biliyan dake Kamfanin buga kudi

- Hannayen jarin na gwamnatin tarayya tana dasu tun fil azal

- An kirkiri Printing and Minting Cpmpany don buga kudi

- Yazo baya iya buga kudin sai an kai kasashen waje

Gwmnatin Tarayya ta sayar wa da babban bankin CBN kudin bashi na N12 biliyan
Gwmnatin Tarayya ta sayar wa da babban bankin CBN kudin bashi na N12 biliyan
Asali: Depositphotos

Gwamnatin Tarayya a Najeriya ta sayar wa da babban bankin Najeriya CBN, hannayen jari har biliyan 12.4 da take dasu a kamfanin wanda shi yake da alhakin buga wa kasar nan takardun kudi da kwandalaye da ake amfani dasu.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci bikin murnar sa hannun sayar da hannayen jarin Gwamnatin tarayya na kamfanin tsaro da buga kudi na Najeriya ga babban bankin Najeriya. Bashin ya kai akalla N12 biliyan.

DUBA WANNAN: Kwamacala a kwangilar rufe Najeriya da rediyo

Shi dai kamfanin NSPM, kamfani ne da tuni ya daina iya buga kudi a Najeriya, sai ya kai kasashen waje, amma daga baya aka tayar da komadarsa, inda yakan buga wasu daga cikin kudaden.

Har ta kai ba'a iya amfani da kwandalaye a NAjeriya, saboda kudin da ake kashewa wajen kera su ya fi karfin darajar su, inda mutane suka koma sayensu su narka suyi amfanin gabansu dashi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel