Binciken yadda MTN ke kwashe biliyoyi daga Najeriya

Binciken yadda MTN ke kwashe biliyoyi daga Najeriya

- An sanya wa MTN takunkumai da kuma tara

- MTN na kwashe kudadenta ba bisa kaida ba zuwa kasashen waje

- Wasu manyan bankuna ke taya ta wannan badakala

Binciken yadda MTN ke kwashe biliyoyi daga Najeriya
Binciken yadda MTN ke kwashe biliyoyi daga Najeriya
Asali: Instagram

Tattalin arziki dai ya ta'allaka ne da yadda kasa ke iya ajje kudade a cikin gida, kirkirar ababen sayarwa ga kasashen waje, shigo da jari da kuma samar da tsaro da saukin yin kasuwanci a cikin kasa. Wannan ne ya sanya wasu kasashen suka yi wa wasu fintinkau.

An gano ashe kamfanin Sadarwa na MTN, wanda ya zo ya zuba jari a cikin Najeriya shekaru kusan 20 da suka wuce, wanda kuma yake cin uwar riba, yanzu ya sami hanyar zirarar da kudinsa zuwa gida Afirka ta kudu, mai fama da matsin tattalin arziki.

Babban bankin CBN, ya gano cewa kamfanin ya fitar da $8b daga NAjeriya a cikin shekaru biyu daga 2016.

DUBA WANNAN: Dakwalen kaji da Najeriya ta samar wa duniya ta hanyar kimiyya

Yana wannan aika-aika ne wadda ke durkusar da tattalin arzikin kasar nan inda yake ajje kudaden a wasu bankuna masu rassa a kasashen waje, sai ya zare kudin daga wadancan bankunan a wata kasar yaje ya biye abinsa.

Yanzu dai bayan ya dawo da kudin cikin Najeriya, kamfanin MTN din zai kuma biya tarar kusan tiriliyan daya na nairori ga gwamnati, lamari da kamfanin yace cin zali ne, domin ya gama biyan wannan kudin a bara biyu.

Sai kuma batun suma dama MTN sunyi kaurin suna waje sace wa 'yan Najeriya kudi a wayarsu, da sunan wai ai ka sayi waqa ko data saboda kawai ka taba saya sau daya, lamari da sai yanzu suke kokarin gyara wa a kwamfiyutarsu, amma basu biya kowa ko sisi ba, watakil gara ma kenan a caje su su baiwa gwamnati makudan kudaden, ko talaka rya rama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel