Jirgin bincike na dakarun Rasha ya bata a teku

Jirgin bincike na dakarun Rasha ya bata a teku

Rahotanni dake zuwa mana sun nunacewa wani Jirgin bincike na dakarun sojin Rasha ya bace a tekun Mediterranean dauke da sojojin kasar su 14.

Kafar yada labaran Rashar ta ce kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar a Moscow ta shaida, jirgin ya bata ne a hare-hare da Isra'ila ta kai ta sama akan asar Syria.

Hakazalika jirgin Rashar ya gano wata roka da aka harba daga jirgin ruwan yakin Faransa.

Jirgin bincike na dakarun Rasha ya bata a teku
Jirgin bincike na dakarun Rasha ya bata a teku
Asali: Depositphotos

Wannan al'amari na zuwa ne adaidai lokacin da Rasha da Turkiya suka amince su kafa yankin tudun mun tsira tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a lardin Idlib na Syria.

A wani lamari na daban, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta halasta shan tare da amfani da tabar wiwi bayan daukan tsawon lokaci ana tafka muhawara akan dacewar haka ko akasinsa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP

Kamfanin jaridar TheCables ce ta ruwaito wannan labari, inda tace babbar kotun kundin tsarin mulki ta kasar ce ta halasta sha da amfani da wiwi, bayan wata kotu a kasar ta yanke hukuncin halast yin amfani da wiwi a gida a shekarar 2017.

Sai ga shi a ranar Talata, 18 ga watan Satumba babbar kotun kasar tace: “Ba zai zama laifi ba idan har mutum baligi yayi amfani da tabar wiwi a gida ba.” Inji Alkali mai sharia Raymond Zondo a yayin da take yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel