Rikici ya barke a tsakar gidar Kwankwasiyya game da fidda dan takarar Gwamna

Rikici ya barke a tsakar gidar Kwankwasiyya game da fidda dan takarar Gwamna

A yanzu haka ana cikin zaman dar dar a tsakanin mabiya tafiyar Kwankwasiyya dake karkashin jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwso a sakamakon kunnowar wata babbar rikici game da dan takarar gwamnan jahar Kano.

Legit.ng ta ruwaito wannan bahallatsa na neman bullowa ne bisa bambamcin ra’ayi dake bayyana tsakanin yan Kwankwasiyya da jagoran Kwankwasiyya game da wanda Kwankwasiyya zata tsyar dan takararta a jam’iyyar PDP don karawa da gwamnan jahar Kano Ganduje a zaben 2019.

KU KARANTA: Addu'ar lashe zabe: Wasu 'yan Kwankwasiyya sun gudanar da Sallah, saukar al'qur'ani da yanka

Rikici ya barke a tsakar gidar Kwankwasiyya game da fidda dan takarar Gwamna
Kwankwasiyya
Asali: UGC

Sanannanun matasa mabiya kuma yan gani kashenin Kwankwasiyya sun bayyana rashin amincewarsu da takarar tsohon mataimakin gwamnan jahar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, wanda shi ake ganin Rabiu Kwankwaso ke kokarin tsayar da shi.

Wani daga cikin halastattun yayan Kwankwasiyya, Abubakar Muhammad Inuwa ya bayyana cewa: “A shekaru uku da suka gabata, an ci mutuncin yan Kwankwasiyya an wulakantamu don kawai muna Kwankwasiyya, babu abinda Farfesa yayi game da haka don nuna yana tare da Kwankwasiyya sai yanzu da yakeson zama gwamna.

“Ya sharbi romon Gandujiyya, ya yabi Ganduje ya soki tsare tsaren Kwankwasiyya, ba zamu taba yarda ya ci moriyar kokarin da muka dinga yi ba a shekaru uku da suka gabata, kamata yayi a matsayinsa na gogaggen Malami ya tattara ya koma jami’a kamar yadda yayi alkawari a baya.” Inji shi.

Shima wani sanannen marubuci a shafukan sadarwa kuma dan tsatson Kwankwasiyya, Adanan Mukhtar ya bayyana cewa a shirya yake yayi bijire ma Kwankwaso matukar ya tsayar da Farfesa takarar gwamna domin a cewarsa baya son talaka.

Sai dai masana siyasar Kano sun fahimci wannan batu a matsayin hannunka mai sanda da yan Kwankwasiyya ke yi ma Kwankwaso nuni ga dan takarar da suke bukata banda Hafiz, daga cikin wadanda ake ambata akwai Rabiu Sulaiman Bichi akan gaba, Aminu Dabo da Dakta Yunusa Dangwani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel