Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su

Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su

Ministoci 3 ne suka yi murabus don radin kan su tun bayan da shugaba Buhari ya nada su a shekarar 2015. Ministocin sune;

1. Kemi Adeosun: Uwargida Kemi Adeosun ta kasance ministar kudin Najeriya tun watan Nuwamba na shekarar 2015.

Ta yi murabus daga mukaminta ne bayan jaridar Premium Times ta bankado cewar ta gabatar da takardar bautar kasa ta bogi domin a nada ta minista.

Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su
Kemi Adeosun
Asali: Depositphotos

A ranar a Jum'a, 14 ga watan Satumba ne, uwargida Adeosun ta yi murabus daga kujerarta ta Ministar kudi, biyo bayan zarginta da ake yi na amfani da takardar shaidar yin bautar kasa ta bogi.

Wannan zargi ya dauki tsawon lokaci yana yawo a tsakanin jama'a, har sai ranar juma'a da Kemi ta kawo karshen shi ta hanyar sauka daga mukamin.

DUBA WANNAN: Yadda zaku yi maganin amosanin ka

2. Mista Kayode Fayemi: Zababben gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, ya yi murabus ne daga mukaminsa ministan ma'adanai da albarkatun kasa ranar 30 Mayu domin mayar da hankali a kan takarar kujerar gwamna da yake yi a wancan lokacin.

Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su
Kayode Fayemi
Asali: UGC

Kafin nada shi mukamin minista a gwamnatin APC, Mista Fayemi ya zama gwamnan jihar Ekiti daga shekarar 2010 zuwa 2014.

3. Amina Mohammed: Tsohuwar ministar muhalli daga watan Nuwamba na shekarar 2015 zuwa watan Disamba na shekarar 2016.

Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su
Amina Mohammed
Asali: Depositphotos

Amina tayi murabus ne daga gwamnatin shugaba Buhari biyo bayan bayan nada ta a matsayin mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel