Jerin tsaffin Gwamnoni 15 dake rike da Kujeru a Majalisar dattawa
A yau tankade da rairayen jaridar Legit.ng ya kawo ma ku jerin tsaffin gwamnonin da suke rike da madafan iko kan kujerun Sanatoci a majalisar dattawan kasar nan, bayan da suka kammala wa'adin su a kujerun gwamnoni na jihohin su.
A makon da ya gabata jaridar ta Legit.ng ta kawo mu ku jerin sunayen gwamnonin jihohin kasar nan ma su ci a karkashin jam'iyyar APC.
Binciken jaridar ya bayyana cewa a halin yanzu akwai tsaffin gwamnoni 15 da ke rike da kujerun Sanatoci a majalisar dattawa.
Ga jerin sunayen tsafaffin gwamnonin tare da mazabar da suke wakilta a majalisar dattawa kamar haka:
1. Abubakar Bukola Saraki; Sanatan jihar Kwara ta Tsakiya
2. Rabi'u Musa Kwankwaso; Sanatan jihar Kano ta Tsakiya
3. Kabiru Gaya; Sanatan jihar Kano ta Kudu
4. Godswill Akpabio; Sanatan jihar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma
5. Aliyu Magatakarda Wamakko; Sanatan Jihar Sakkwato ta Arewa
6. Abdullahi Adamu; Sanatan jihar Nasarrawa ta Yamma
7. Sam Egwu; Sanatan jihar Ebonyi ta Arewa
8. Muhammad Shaaba Lafiagi; Sanatan jihar Kwara ta Arewa
KARANTA KUMA: Rikici a PDP yayin da amintattun jam'iyya ke bayyana goyan bayan su ga wasu 'yan takara na jam'iyyar
9. Joshua Chibi Dariye; Sanatan jihar Filato ta Tsakiya
10. Jonah Jang; Sanatan jihar Filato ta Arewa
11. Ahmed Sani Yerima; Sanatan jihar Zamfara ta Yamma
12. Danjuma Goje; Sanatan jihar Gombe ta Tsakiya
13. Bukar Abba Ibrahim; Sanatan jihar Yobe ta Gabas
14. George Akume; Sanatan jihar Benuwe ta Yamma
15. Theodore Orji; Sanatan jihar Abia ta Tsakiya
Kazalika akwai kuma wasu tsofaffin mataimakan gwamna dake rike da kujeru a majalisar dattawa da suka hadar da; Mrs Biodun Olujimi ta jihar Ekiti da kuma Enyinaya Abaribe na jihar Abia.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng