Na yi biyayya ta tsawon shekaru 7 cikin jam'iyya daya ba tare da wani nadin mukami ba - Osinbajo

Na yi biyayya ta tsawon shekaru 7 cikin jam'iyya daya ba tare da wani nadin mukami ba - Osinbajo

A ranar Alhamis din da ta gabata ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ya yi biyayya har ta tsawon shekaru bakwai cikin jam'iyyar guda ba tare da samun wata kyautatawa ba ta nadin mukami.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, bai samu nadin wani mukami ba tun bayan da ya kammala jagorancin sa kan kujerar lauyan kolu kuma kwamshinan shari'a na jihar Legas a shekarar 2003 da ta gabata.

Mista Laolu Akande, mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasar shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar da ta gabata.

Na yi biyayya ta tsawon shekaru 7 cikin jam'iyya daya ba tare da wani nadin mukami ba - Osinbajo

Na yi biyayya ta tsawon shekaru 7 cikin jam'iyya daya ba tare da wani nadin mukami ba - Osinbajo
Source: Depositphotos

Osinbajo ya yi wannan furuci ne yayin ganawarsa da matasan manema takara karkashin jam'iyyar su ta APC a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja.

KARANTA KUMA: Matasa sun gudanar da gangami tare da karaɗe jihar Imo domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Buhari

NAIJ.com ta fahimci cewa, Osinbajo ya rike mukamin kwamshinan shari'a na jihar Legas karkashin inuwa ta jam'iyyar AD (Alliance for Democracy) a yayin da Asiwaju Bola Tinubu ke rike da kujerar gwamnatin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, mafi akasari mambobi da suka assasa jam'iyyar AD sun sauya sheka zuwa jam'iyyar AC (Action Congress), inda daga baya ta cure tare da hade kai wajen komawa jam'iyyar APC mai ci kuma a halin yanzu cikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu
NAIJ.com
Mailfire view pixel