Rikicin shugabancin ya kaure tsakanin bangarori biyu na APC a jihar Arewa

Rikicin shugabancin ya kaure tsakanin bangarori biyu na APC a jihar Arewa

- Rikici ta barke tsakanin magoya bayan mutane biyu da ke fada kan kujerar Ciyaman na APC a Taraba

- An samu Ciyamomi biyu ne saboda an zabi na farko zamanin John Oyegun kuma daga baya Ciyaman din jam'iyya, Oshiomhole ya sake gudanar da zabe a jihar

Rikici ta barke tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar APC reshen jihar Taraba bayan wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da sabon Ciyaman din jam'iyyar, Ibrahim Elsuldi daga fara aiki a ofishin jam'iyyar da ke Jalingo.

Alkalin babban kotun, Hon. Justice Valentine Ashi, ya dakatar da Elsudi ne bayan tsohon Ciyaman din jam'iyyar Dr. Abdulmumin Vaki ya shigar da kara kotun inda ya nemi kotun ta soke zaben Elsudi.

Rikicin shugabancin ya kaure tsakanin bangarori biyu na APC a jihar Arewa
Rikicin shugabancin ya kaure tsakanin bangarori biyu na APC a jihar Arewa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An cafke wani matashi yayin da yake lalata allon takarar Buhari (hotuna)

An zabi Vaki ne a matsayin Ciyaman a taron jam'iyyar da akayi kwanakin baya karkashin jagorancin tsohon Ciyaman din APC, John Oyegun yayin da shi kuma Ibrahim an zabe shi ne ranar Litini da ta gabata karkashin jagorancin sabon Ciyaman din APC, Adams Oshiomhole.

A hukuncin da alkalin ya zartar a yanzu, ya umurci Hon. Ibrahim Elsudi ya dena gabatar da kansa a matsayin Ciyaman na jam'iyyar APC na jihar Taraba.

Wannan hukuncin kotun na ya janyo rikici tsakanin mambobin jam'iyyar da ke biyaya ga ministan harkokin mata, Senata Jummai Alhassan, wanda ke marawa Abdulmumini Vaki baya da kuma magoya bayan Ibrahim Elsudi.

Majiyat Legit.ng ta ruwaito cewa 'yan sanda sun mamaye harabar ofishin jam'iyyar na jihar domin hana zubar da jini tsakanin 'yan bangarori biyu na jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel