An cafke wani matashi yayin da yake lalata allon takarar Buhari (hotuna)

An cafke wani matashi yayin da yake lalata allon takarar Buhari (hotuna)

- 'Yan sanda sunyi ram da wani matashi da ke yaga allon takarar shugaba Muhammadu Buhari

- Matashin ya aikata hakan ne wai don bai gamsu da sallon mulkin gwamnati mai ci yanzu ba

- Tuni jami'an 'yan sandan sun tisa keyar matashin zuwa caji ofis domin gurfanar dashi a kotu

Mun samu daga National Helm cewa jam'ian 'yan sanda da ke babban birnin tarayya Abuja sun kama wani matashi da aka samu da rana tsaka yana lalata allon takarar shugaba Muhammadu Buhari.

An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
Asali: Twitter

An gano matakin ya yanke shawarar lalata allon takarar ne saboda wai bai gamsu da yadda harkoki ke tafiya a kasar ba sai dai hakan bai hana 'yan sanda tisa keyarsa ba.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP

An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
Asali: Twitter

A watan Augusta da ta gabata, hukumar 'yan sandan jihar Kano sunyi gargadi cewa duk wani da aka samu yana lalata fostan takarar shugaba Muhammadu Buhari zai fuskanci fushin hukuma.

Yan sandan sun bayar da wannan sanarwan ne bayan an samu wasu matasa na lalata fostoci ta hanyar yage su ko kuma kwakwule sassan hoton da ake kyautata zaton 'yan jam'iyyun adawa ne ke aikata hakan.

An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
An yi ram da wani matashi yayin da yake tsaka da lalata allon takarar Buhari
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Magaji Majia ya ce hukumar ba baza jami'anta masu saka unifom da masu saka kayan farar hula domin sa ido kan wadanda ke lalata fostoci a sassan jihar ta Kano.

A cewar Majia, ya zama dole a dauki tsatsauran mataki bayan wasu bata gari da ba'a san ko su wanene ba sun lalata allon takarar shugaba Buhari da ke kan titin Sharada a Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel