Ba na shakkar yin fito-na-fito da Kwankwaso - Shekarau

Ba na shakkar yin fito-na-fito da Kwankwaso - Shekarau

Kamar yadda rahotanni suka bayyana da sanadin kafofin watsa labaru da dama na kasar nan, mun samu rahotan cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya daura damarar tsayawa takarar kujerar Sanatan Jihar Kano ta Tsakiya.

Ko shakka babu a halin yanzu tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, shine ke rike da wannan Kujera da Mallam Shekarau ke hankoro wanda da dama ke hasashen sai an kai ruwa rana wajen fafata wannan takara.

Kwankwaso wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP yayin da guguwar sauyin sheka ta kada a kasar nan, ya na kuma neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP wanda Hausawa kan ce da tsohuwar Zuma ake magani.

Ba na shakkar yin fito-na-fito da Kwankwaso - Shekarau
Ba na shakkar yin fito-na-fito da Kwankwaso - Shekarau
Asali: Depositphotos

Kazalika, a yayin da sauyin sheka ya zamto ruwan dare a kasar nan inda 'yan siyasa ke faman shige da fice ba bu kama hannun yaro, Shekarau wanda a karshen makon da ya gabata shi ma ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa tsohuwar jam'iyyar sa ta APC, zai kuma tsaya takarar kujerar da Kwankwaso ke kai a halin yanzu.

Sai dai Mallam Shekarau ya bayyana cewa, bai sauya sheka zuwa jam'iyyar ta APC ba bisa ga kwadayin wata kujera inda tuni ya ajiye sha'awarsa ta takarar kujerar shugaban kasa wanda a baya ya kudirta yayin da yake jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Mu na da tabbatattun mambobi 15.6m masu rijista ta jam'iyyar APC - Oshiomhole

Ya ci gaba da cewa, ya yanke shawarar tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a sanadiyar matsantawa da kuma rokon shugabannin jam'iyyar sa ta APC da a baya ba ya da wata sha'awa akan hakan.

Shekarau ya kara da cewa, sai dai a halin yanzu ba ya jin wata fargaba ta yin fito-na-fito da kowane dan siyasa ta fafata takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, ko da kuwa Kwankwaso zai sake neman tazarce a kanta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel