Tarihi: Birgediya Zakariya Maimalari, kwararren jami’in soja na farko a Najeriya

Tarihi: Birgediya Zakariya Maimalari, kwararren jami’in soja na farko a Najeriya

Lallai aikin soja na da dadaden tarihi a kasar Najeriya dama duniya baki daya. Sojoji su dade suna bayar da gudunmawarsu tare da jajircewa wajen kare kasarsu da al'umman kasar da kuma dukiyoyin jama'a.

Ba'a bar kasar Najeriya a baya ba wajen samun nagartattun sojoji masu kwazo da sanin makamar aiki, don haka muka kawo maku tarihin daya daga cikin wadannan jaruman.

Birgediya Zakariya Maimalari ya kasance daya daga cikin yan Afrika nafarko da aka horar a makarantar soji na British Royal Military Academy a Sandhurst dake Amurka.

Ka san Birgediya Zakariya Maimalari kwararren jami’in soja na farko a Najeriya?
Ka san Birgediya Zakariya Maimalari kwararren jami’in soja na farko a Najeriya?
Asali: Depositphotos

Ya kuma kasance kwararen jami’in soja na farko a gida Najeriya.

Amma a watan Janairun 1966 kananan jami’an soji suka kashe shi a lokacin juyin mulkin Najeriya na farko wanda a cikinta ne John son Aguiyi-Ironsi ya hau mulki.

KU KARANTA KUMA: Masarautar Kano na shirin fitar da doka akan yawaitar mutuwar aure

A bisa wani rubutaccen tarihi ndaga Haruna Yahaya Poloma mai suna ‘The First Regular Combatant, Brigadier Zakariya Maimalari’ ya nuna cewa Maimalari shine mutun na fako dayayi karatun Boko a gidansu kuma ya kasance dalibi mai kwazo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel