Tursasa ni aka yi ina zaman lafiya na na shigo cikin siyasa – Buhari

Tursasa ni aka yi ina zaman lafiya na na shigo cikin siyasa – Buhari

A makon nan ne Shugaba Buhari ya karbi fam din sa na sake neman takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC a zaben 2019. Tuni dai har Shugaban ya maida fam din bayan ya cike a Hedikwatar Jam’iyyar a Abuja.

Tursasa ni aka yi ina zaman lafiya na na shigo cikin siyasa – Buhari
Shugaba Buhari ya bada labarin yadda su ka sha wuya a rayuwar siyasa
Asali: Instagram

Mun kawo kadan daga cikin jawabin Shugaban kasar lokacin da ya mikawa Jam’iyya fam din na sa.

1. Shigowa cikin siyasa

Shugaba Buhari ya bayyana cewa wasu Bayin Allah ne su ka matsa masa yayi aikin PTF da Gwamnatin Abacha har kuma ya shigo siyasa bayan yayi ritaya yana zaune a gidan sa a Garin Kaduna. Buhari yace a lokacin abubuwa sun tabarbare ainun a kasar.

KU KARANTA: Jonathan ya saka alamar tambaya a kan lafiyar Oshiomhole

2. Murde zabukan 2003, 2007 da 2011

Buhari ya kuma bada labarin yadda Jam’iyyar PDP ta rika aringizo a zabukan da aka yi tun daga 2003 zuwa 2011. Buhari yace Duniya ta sallama cewa ba ayi zaben kwarai ba. Shugaban kasar ya tunawa mutane yadda su ka rika fama a Kotun koli amma ba su yi nasara ba.

3. Mulkin Jonathan da zaben 2015

Shugaban kasar ya kuma yi magana game da mulkin Jonathan inda ya bayyana cewa duk da karfin tattalin arzikin da aka ce Najeriya tayi sai da ta kai ana cin bashi wajen biyan albashi a kasar. Buhari yace sai a zaben 2015 ne da aka yi amfani da fasaha na zamani su ka lashe zabe.

Kwanaki kun ji cewa Kwamitin yakin neman zaben Buhari ya bayyana cewa karo-karo aka yi wajen sayawa Shugaba Muhammadu Buhari fam din sake takarar Shugaban kasa a zaben badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel