Matar babban sojan nan da ya bace yai magana game da mijin na ta

Matar babban sojan nan da ya bace yai magana game da mijin na ta

- Matar babban sojan nan da ya bace sati 2 da suka wuce tayi magana game da mijin na ta

- Manjo Janar Idris Alkali wanda yanzu saura 'yan kwanaki kadan ya yi ritaya

Matar sojan nan mai suna da ya bace kimanin sati biyu da suka shude a kan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja mai suna Salamatu Alkali tayi magana game da mijin nata, kamar dai yadda majiyar mu ta jaridar Daily Nigerian ta sanar mana.

Matar babban sojan nan da ya bace yai magana game da mijin na ta
Matar babban sojan nan da ya bace yai magana game da mijin na ta
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ambode yayi karin haske game da rikicin sa da Tinubu

Kamar dai yadda muka samu, Manjo Janar Idris Alkali wanda yanzu saura 'yan kwanaki kadan ya yi ritaya, ya bace ne akan hanyar sa ta zuwa gonar sa a garin Bauchi daga gidan sa a Abuja.

Legit.ng ta samu cewa matar ta sojan ta ce lokaci na karshe da tayi magana da mijin nata shine lokacin da zai yi tafiyar inda ya fada mata cewa yana so yabi ta hanyar Jos inda ita kuma tace kamata yayi yabi ta Kaduna saboda rashin kyaun hanyar.

Sai dai ta kuma bayyana cewa mahukunta a rundunar sojin kasar sun tabbatar mata da cewa tuni aka sa manyan jami'an su na musamman domin gano inda yake.

Tace tabbas su na cikin damuwa sosai tun bayan bacewar tashi domin har yanzu basu san halin da yake ciki ba.

A wani labarin kuma, Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel