Gwamna Ambode ya yi karin haske game da rikicin sa da Cif Bola Tinubu

Gwamna Ambode ya yi karin haske game da rikicin sa da Cif Bola Tinubu

- Gwamna Ambode ya yi karin haske game da rikicin sa da Cif Bola Tinubu

- Wannan dai na a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun hadimin sa

- Yace duk karya ce da labarin kanzon kurege

Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode a ranar Laraba ya yi karin haske game da rikicin da ake rade-raden ya shiga tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), mai mulki watau Cif Bola Tinubu.

Gwamna Ambode ya yi karin haske game da rikicin sa da Cif Bola Tinubu
Gwamna Ambode ya yi karin haske game da rikicin sa da Cif Bola Tinubu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wata mace ta baiwa maza shawarar su kara aure a Najeriya

A cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar ta Legas mai suna Habib Aruna, Gwamna Akinwunmi Ambode yace duk karya ce ake ta yada wa game da batun amma a hakikanin gaskiya babu wata rashin jituwa da ta shiga tsakanin su.

Legit.ng ta samu cewa kafofin yada labarai na yanar gizo da ma wadanda ake bugawa a cikin satin da ya gabata da kuma farkon wannan da ake ciki dai sun yi ta ruwaito labarin cewa babbar matsala ta shiga tsakanin gwamnan da tsohon uban gidan na sa.

A wani labarin kuma, Mun samu labarin cewa an tashi ba'a cimma matsaya ba a wani zaman sasanci da aka so yiwa 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kamar dai yadda muka samu, taron wanda aka gudanar a ofishin uwar jam'iyyar a garin Abuja ya samu halartar shugaban jam'iyyar ta PDP Cif Uche Secondus, gwamnonin jam'iyyar ta PDP da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel