Sabon salo: PDP ta zo da sabon tsari a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa

Sabon salo: PDP ta zo da sabon tsari a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa

- A ranar 6 ga watan Oktoba ne jam’iyyar PDP ta sanar da cewar zata gudanar da zaben cikin gida na fitar da ‘yan takara

- PDP ta ce zata gudanar da zaben fitar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar saka hoton kowanne dan takara a akwatin saka kuri’a

- Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, ya bayyana hakan yau, Laraba, a Abuja yayin taro da gamayyar kungiyar Turai (EU)

Jam’iyyar PDP ta ceta fito da sabon tsari na makala hoton ‘yan takarar shugaban kasa a jikin akwatinan kada kuri’a da za a yi amfani da su yayin zaben fitar da gwani da za a yi ranar 6 ga watan oktoba.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, ya sanar da haka a yau, Laraba, yayin ganawa da wakilan gamayyar kungiyar Turai (EU) karkashin jagorancin Bridget Markussen a ofishinsa dake Abuja.

Sabon salo: PDP ta zo da sabon tsari a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa
'Yan takarar PDP
Asali: Depositphotos

Secondus ya shaidawa wakilan na EU cewar har yanzu jam’iyyar PDP na kokarin kafa kwamitin da zai gudanar da zabukan cikin gida.

Kazalika ya shaida masu cewar dukkan ‘yan takarar 13 zasu bayar da wakilansu a cikin kwamitin da gudanar da zaben da jam’iyyar zata kafa.

DUBA WANNAN: 2019: Tinubu ya tsayar da dan takarar gwamna a Legas, ya juyawa Ambode baya

Muna kokarin kafa kwamitin da zai gudanar da zabe nan bada dadewa ba domin mu mika masu harkar gudanar da zaben fitar da ‘yan takara.

Dukkan ‘yan takarar mu na shugaban kasa 13 zasu bayar da wakilai a cikin kwamitin da za a kafa. Zamu fitar da tsarin tantance daliget da zasu kada kuri’a domin tabbatar da an yi zabe da babu wanda zai korafin an tauye shi,” a kalaman Secondus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel