Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna

- A ranar juma’ar makon jiya ne tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya canja sheka daga PDP zuwa APC

- Shekarau ya yanki katin shaidar zama mamba a jam’iyyar APC ranar Lahadi a mazabarsa dake unguwar Giginyu a karamar hukumar Nasarawa

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi tattaki ya zuwa jihar Kano domin yiwa Shekarau murnar dawowa APC

A yau, Laraba, ne gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ziyarci Kano domin taya tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, murnar canjin shekar da ya yi daga PDP zuwa APC a satin da ya gabata.

Rochas da Shekarau sun gana ne a fadar gwamnatin Kano, kuma gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya kasance mai masaukin baki.

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Ganduje, Shekarau da Rochas
Asali: Facebook

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Asali: Facebook

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Asali: Facebook

Da yake bayyana dalilinsa na fita daga PDP, tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC.

DUBA WANNAN: 2019: Sanata, tsohon mataimakin gwamna da DIG mai ritaya sun koma APC a jihar PDP

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa.

A karshe, Malam Ibrahim Shekarau, ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa ta Giginyu a karamar hukumar Nasara dake Kano a ranar Lahadi.

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Ganduje, Shekarau da Rochas
Asali: Facebook

Takanas-ta-kano: Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Gwamnan APC ya yi tattaki har Kano don yiwa shekarau murna
Asali: Facebook

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel