Ni da fina-finan Hausa, mutu ka raba -Jamila Nagudu

Ni da fina-finan Hausa, mutu ka raba -Jamila Nagudu

Shahrarriyar jarumar wasan kwaikwayon Hausa wato Kannywood, Jamila Umar Nagudu, ya bayyana niyyar cigaba da harkar fim har sai lokacin da Allah ya dauki ranta.

Jamila Nagudu wacce ke cikin jaruman Kannywood mafi dadewa a harkar fim a yanzu kuma wacce auraruwarta ke haskawa tun shigowarta har rana mai kamar yau kuma cikin jarumai mata mafi arziki a harkar fim.

Ta samu makudan kudi sakamakon shahararta ta hanyar tallace-tallacen da takewa kamfanonin Najeriya da wasu kasashen da ke makwabta.

Tun lokacin da aurenta ya mutu a jihar Bauchi, bata nuna niyyar sake aure ba musamman bayan ta kafu a masana’antar fina-finan Hausa.

Ni da fina-finan Hausa, mutu ka raba -Jamila Nagudu

Ni da fina-finan Hausa, mutu ka raba -Jamila Nagudu
Source: Facebook

KU KARANTA: Zan kawo kaina ofishinku ranan 16 ga watan Oktoba – Fayose ga EFCC

Rashin auren jamila nagudu yana kada hanjin wasu daga masoyanta wadanda suke burin ganin ta sake aure saidai kuma watakila ita ta hango wani abinda basu hango ba acikin komawa rayuwar aure gareta.

Jamila Nagudu tanada yara wadanda ta kafa dayawa acikin masana'antar Kannywood tun daga kan daraktoci, furodusoshi dama jarumai mata da maza wadanda sukaci albarkacinta.

Jarumai mata dayawa a kannywood sun cirewa kansu zancen aure saboda yadda mazaje ke aurensu don bukata kawai daga baya a sakesu. Wannan shine babban kalubale dayake addabar mata masu shigowa masana'antar fina finai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani matashi da ya yiwa mata shida fyade ya shiga hannun hukuma

Wani matashi da ya yiwa mata shida fyade ya shiga hannun hukuma

Wani saurayi da ya danne 'yan mata shida ya shiga hannun hukuma
NAIJ.com
Mailfire view pixel