Yadda zamu yi da kudaden da muka kwato daga hannun 'yan wawaso - Buhari

Yadda zamu yi da kudaden da muka kwato daga hannun 'yan wawaso - Buhari

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za tayi amfani da kudaden da aka kwato daga masu wawuso domin yiwa al'umma aiki

- Shugaban kasa ya kuma ce gwamnatinsa na daukan matakan dakile guraben da ake amfani da su wajen sata

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa tana gab da kafa doka da zata karfafawa gwamnati wajen kwato kudade daga barayin gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za tayi amfani da kudaden da gwamnatinsa da kwato daga hannun wadanda suka wawushe kudaden jama'a wajen gudanar da ayyukan more rayuwa da cigaban al'umma.

Yadda zamu yi da kudaden da muka kwato daga hannun 'yan wawaso - Buhari
Yadda zamu yi da kudaden da muka kwato daga hannun 'yan wawaso - Buhari
Asali: Facebook

Shugaban kasa ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a fadar Aso Villa yayin da ya karba rahoton kwamitin da aka kafa domin tantance adadin kudaden da gwamnatin ta karbo. Ya kuma ce dole ne a dakile hanyoyin da masu wawuran kudaden ke sata.

DUBA WANNAN: Zaben fidda gwani: Shehu Sani da wasu 'yan takara 14 sun yiwa APC tawaye a Kaduna

Buhari ya ce gwamnatinsa ba zata amince wasu tsiraru su rika karkatar da kudaden jama'a zuwa aljihunsu ba.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta cigaba da daukan matakan toshe hanyoyin da masu wawure kudade ke amfani dashi wajen satar kudaden.

Kazalika, shugaban kasan ya ce gwamnatinsa tana aiki kan doka da za ta tabbatar da hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen sace kudaden al'umma, inda ya kara da cewa dokar tana gaban majalisar tarayya.

"Da zarar an amince da dokar, yawancin matsalolin da ake fuskanta wajen kwato kudaden da barayin gwamnati suka wawure a Najeriya za su gushe," inji shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa ya yi kira ga majalisar tarayya ta gagauata amincewa da kudirin dokar saboda ta zama doka a fara amfani da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel