Yan majalisar wakilai 23 na shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yan majalisar wakilai 23 na shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Mambobin majalisar wakilai a jam'iyyar PDP 23 na shirin sauya sheka zuwa APC

- Hakan ya biyo bayan rashin jituwa da aka ce ya shiga tsakaninsu da gwamnoninsu

- An yi zargin cewa APC ta shirya basu tikitin tazarce domin ta janyo hankalinsu zuwa jam'iyyarta

A ranar Talata, 11 ga watan Satumba mun samu labarin cewa akalla mambobin majalisar wakilai 23 a karkashin jam’iyyar PDP ne suke shirin sauya sheka daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu shirin sauya shekan sun nuna bacin ransu game da yadda gwamnoninsu ke gudanar da al’amura wato gabatar da sabbin masu takara a maimakon yan majalisa dake ci.

Jihohi dake shirinfuskantar sauya shekan sun hada da Gombe, Benue, Kogi, Enugu, Ekiti, Anambra, Cross River, da saura wadanda yan majalisunsu ke samun rashin jituwa da gwamnoninsu.

Yan majalisar wakilai 23 na shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yan majalisar wakilai 23 na shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC
Source: Depositphotos

Wata majiya gabannin shirye shiryen sauya shekan ta bayyana cewa, ga dukkan alamu akwai tangarda a jam’iyyar PDP, ba a cimma nasara ba a tattaunawar kwamitin dake kula da tabbacin gudanar da zaben fidda gwani a fadin jihohin.

Majiyar ta cigaba da bayyana cewa jam’iyyar APC tana shirin baiwa yan majalisa da suka fusata tikiti kai tsaye don janyo su jam’iyyarsu.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 11 ga watan Satumba ya bayyana cewa yan siyasa masu rauni sun bar jam’iyyar All Progressives Congress, (APC).

Buhari na hannunka mai sanda ne ga yan siyasa da dama da suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyun adawa.

Yayi maganan ne yayinda ya karbi fam din sake tsayawa takara da kungiyar Nigeria Consolidation Ambassador Network (NCAN) ta siya masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Wulakanci: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun
NAIJ.com
Mailfire view pixel