Sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa

Sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa

- Sojin sama sun yi raga-raga da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram

- Ma'ajiyar makaman 'yan ta'addan dai na a maboyar su dake a dajin Sambisa

Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa
Sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan majalisa sun canza ranar dawowa hutu

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na jami'an kuma mai magana da yawun su, Air Commodore Ibikunle Daramola shine ya sanarwa da manema labarai hakan a hedikwatar rundunar sojin saman dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, Abuja.

Air Commodore Ibikunle Daramola ya kara da cewa wani bincike sirri ne da jami'an su suka gudanar a sararin samaniya suka gano maboyar makaman na 'yan Boko Haram kafin daga bisani su shirya su kuma kai masu hari.

A wani labarin kuma, Babban kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ce tuni yayi nisa wajen ganin ya kwantar da dukkan wata fitina da ka iya tasowa zaben fitar da gwanin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a ranar 6 ga watan Okotoba mai zuwa.

Shugaban kwamitin amintattun, Sanata Walid Jibrin shine ya sanar da hakan a garin Abuja, ranar Litinin din da ta gabata inda ya bayyana cewa kawo yanzu dai suna ta kokarin ganin 'yan takarar dukkan su sun amince da sasancin da zai fito da mutum daya a tsakanin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel