Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan

- Fadar Sarkin musulmi, Sa'ad Abubakar II, tayi tsokaci kan hatsatrin da ya ritsa da dan sultan a jiya

- Fadar Sarkin musulmin ta ce Amir Sa'ad Abubakar da 'yan uwansa biyu suna samun sauki cikin gagawa

- Fadar sarkin musulmin kuma ta mika godiyarta ga wadanda suka ta mika gaisuwarsu ga Sarkin musulmi da iyalansa

Fadar Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar II, da ke Sakkwato ta bayar da sanarwar cewa 'dan Sultan, Amir Sa'ad Abubakar da 'yan uwansa biyu da hatsarin mota ya ritsa da su a jiya sana samun sauki cikin gagawa.

Amir ya yi hatsarin da mota ne misalin karfe 12 na rana wajen filin jirgin saman jihar Sokoto. Ya kasance yana tare da dan uwansa Khalifah Muhammad Maccido da Zainab Bara'u Isah a cikin motar.

Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan
Fadan sarkin musulmi tayi tsokaci kan hatsarin 'dan Sultan
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

"Fadar Sarkin musulmi tana farin cikin sanar da cewa Amir Sa'ad Abubakar wanda aka kwantar a asibiti a jiya dalilin raunin da ya yi bayan ya yi hatsarin mota tare da 'yan uwansa biyu, Khalifa Muhammad Maccido da Zainab Bara'u Isah suna samun saukin cikin gagawa," inji sanarwan.

Sanarwan mai dauke da sa hannun sakataren Fadan sarkin musulmin, ta kara da cewa, "Tun bayan afkuwar hatsarin a ranar Lahadi, mutane da dama suna ta tururuwa domin gaisuwa ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar CFR, da iyalansa da 'yan uwansa tun bayan da labarin ya bazu a kafafen sada labarai.

"Ina son amfani da wannan daman domin tabbatar wa jama'a cewa wadanda hatsarin ya ritsa da su suna samun kulawar da ta kamata kuma suna samun sauki sosai."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel