Mai laya kiyayi mai zamani: Yarima ya janye daga takarar Sanata bayan fitowar gwamna Yari

Mai laya kiyayi mai zamani: Yarima ya janye daga takarar Sanata bayan fitowar gwamna Yari

Gwamnan jihar Zamfar, Abdulaziz Yari, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Sanata da zai wakilicin yammacin Zamfara a majalisar dattijai.

Da yake ganawa da manema labarai yau, Litinin, a Gusau, gwamna Yari y ace zai yi takarar ne saboda sha’awar da yake da ita na son zama mai yin doka da zasu amfani jama’a.

Ni dama dan majalisa ne, daga can na fara siyasa saboda haka zan koma gida ne. ko abokaina a majalisa kan fada min cewar zama na a kujerar gwamna tamkar naje hutu ne domin zan dawo cikinsu,” a kalaman Yari.

A ya yin da wasu ke ganin gwamna Yari zai fafata neman kujerar ne da tsohon maigidansa, Sanata Abdullahi Sani Yarima, sai gas hi jaridar Tribune ta rawaito cewar Yariman ya janyewa gwamna Yari takarar kujerar sanatan yankin da suka fito, yammacin jihar Zamfara.

Mai laya kiyayi mai zamani: Yarima ya janye daga takarar Sanata bayan fitowar gwamna Yari
Gwamna Yari
Asali: UGC

Alamun janyewar ta Yarima sun bayyana ne bayan kamala wani zama da manyan APC suka yi a jihar Zamfara in da gwamna Yari ya zabi kwamishinan san a kudi, Muktar Idris, a matsayin wanda zai yiwa jam’iyyar takarar gwamna.

DUBA WANNAN: 2019: 'Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya yiwa dabaibayi

Gwamnan ya shaidawa manyan ‘yan jam’iyyar cewar shine dan takarar sanata na yammacin Zamfara tare da shaida masu cewar su taya shi yin godiya ga maigidansa, Sanata Yarima, day a hakura ya bar masa takarar kujerar.

Sanata Yarima ya shafe tsawon shekaru 11 yana wakiltar yammacin jihar Zamfara bayan ya kamala zango biyu a matsayin gwamna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel