Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

- Akalla mutane bakwai ne suka siya fam din takarar kujerar gwamna karkashin APC a jihar Nasarawa

- Haka zalika yan takara biyar sun yanki fam din wannan kujera a karkashin PDP

- A yanzu dai ana da yan takarar kujerar gwamna 12 daga bangarorin guda biyu a jihar

Yan takaran kujerar gwamna guda bakwai karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yanki fam din takara a jihar Nasarwa, jaridar Leadership ta ruwaito.

Yan takaran da suka siya fam din sun hada da mataimakin gwamnan jihar mai ci a yanzu, Silas Ali Agara, Abdullahi A. Sule, da Architect Ibrahim Jaafaru, mamba mai wakiltan mazabar Nasarawa da Toto a majalisar dokokin kasar.

Sauran sun hada da Aliyu Ahmed Wadada, tsohon mamban majalisar wakilai, Alhaji Danladi Halilu Evulanza, tsohon jami’in hukumar shari’a na saka (NJC), Alhaji Dauda Shuaibu Kigba, sakataren gwamnatin tarayya mai ritaya da kuma Alhaji Zakari Idde, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, sashin arewa maso tsakiya.

Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa
Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa
Asali: Depositphotos

Gaba daya yan takara 17 ne suka nuna ra’ayin takarar wannan kujera a APC a jihar. Wata majiya daga sakatariyar APC na jihar ta nuna cewa ana sanya ran Karin yan taakaran da zasu yanki fam, bayan kara wa’adin ranakun siyan fam din da aka yi.

A halin da ake ciki, biyar daga cikin yan takaran kujerar gwamna shida na PDP a jihar sun yanki fam dinsu.

KU KARANTA KUMA: Garba Shehu yace adawa ne yasa aka zargi Kyari da cin hanci

Sune Sanata Phillip Aruwa Gyunka, sanata mai wakiltan yankin Nasarawa ta arewa a majalisar dattawa, Sanata Solomon Ewuga, tsohon karamin ministan Abuja, Dameshi Luka, tsohon mataimakin gwamna, Sanata Patricia Akwashiki, tsohuwar ministar bayanai da David Emmanuel Ombugadu, mamba mai wakiltan Akwanga, Wamba da kuma Narawa Eggon a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel