Tsaka mai wuya: ‘Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya hana samun farinjini

Tsaka mai wuya: ‘Yan takarar PDP 6 da zargin cin hanci ya hana samun farinjini

A kidaya ta karshe da aka yi, akwai mutum 14 dake takarar neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa.

‘Yan takarar su ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark; shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo; tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa; tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi.

Ragowar sun hada da tsohon gwamnan jihar Filato, David Jang; tsohon ministan aiyuka na musamman, Tanimu Turaki; da kuma tsohon sanatan jihar Kaduna ta arewa, Datti Baba-Ahmed.

Sai dai da yawa daga cikin ‘yan takarar na fama da zarge-zarge da tuhumar cin hanci, hakan ya saka shakku a zukatan ‘yan Najeriya wajen kada kuri’a ga irin wadannan takara.

Atiku Abubakar: Akwai zarge-zargen cin hanci masu yawa da karfi a kan tsohon mataimakin shugaban kasa lokacin da ya kasance mataimakin shugaban kasa na tsawon shekara 8.

Wani kwamiti da majalisar dattijai ta kafa a 2006 a karkashin jagorancin Victor Ndoma-Egba ya ce ya samu Atiku da tsohon shugaba Obasanjo da badakala da kudaden man fetur.

Bukola Saraki: Saraki, Tsohon gwamna na tsawon shekara 8 jihar Kwara, na fusakantar zarge-zargen cin hanci da suka hada da yin karyar bayyana abinda ya mallaka da kuma yin amfani da kudaden daga asusun jihar Kwara wajen kafa wasu kamfanoni a kasashen ketare.

An gurfanar da Saraki gaban kotun da’ar ma’aikata bisa tuhumar sa da aikata laifuka 13 masu nasaba da cin hanci da yin karya da gan-gan.

David Mark: Shine Sanatan mafi dadewa a majalisar dattijan Najeriya. Tun shekarar 1999 yake wakiltar jihar Benuwe ta kudu a majalisar dattijai.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Mark a gaban kotu a watan Disamba na shekarar 2017 da watan Janairu na 2018 bisa zarginsa da karbar wasu makudan kudi ta haramtacciyar hanya gabanin zabukan shekarar 2015.

Sule Lamido: Ba da dadewa ba bayan ya bar kujerar gwamnan jihar Jigawa, wata kotu ta tisa keyar Lamido zuwa gidan yari bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi bisa zarginsa da cin hanci da almundahana.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Lamido gaban kotu tare da ‘ya’yansa bisa tuhumar su da badakala da karkatar da kudin mutanen jihar Jigawa.

Attahiru Bafarawa: kwanan nan wata kotu a jihar Sokoto tayi sohon watsi da karar da EFCC ta shigar da Bafarwa bayan fiye da shekara 7 ana fafata shari’a.

Sai dai hukumar EFCC ta ce ba zata gajiya ba har sai ta tabbatar Bafarawa ya girbi abinda ya shuka na yin sama da fadi da kudin gwamnatin jihar Sokoto da yawansu ya kai biliyan N15bn.

Jonah Jang: Dattijo mai shekaru 74 na fuskantar tuhumar cin hanci na biliyan N6.3bn, kudin da hukumar EFCC ta ce ya kwashe su ne daga asusun Filato, jihar da ya mulka daga 2007 zuwa 2011.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel