Zaben fidda gwani: An fara rikici tsakanin Gwamnoni da Shugaban jam'iyyar APC

Zaben fidda gwani: An fara rikici tsakanin Gwamnoni da Shugaban jam'iyyar APC

Mun samu cewa wakilai ma su fidda 'yan takara na jam'iyyar APC a mazabu da kuma kananan hukumomi, sun bayyana rashin amincewar su kan zaben 'yar tinke da da shugaban jam'iyyar, Kwamared Adams Oshiomhole, ke kokarin dabbakawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban jam'iyyar, Sanatoci da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, su na goyan bayan aiwartar da zabe na 'yar tinke yayin zaben fidda gwanaye na jam'iyyar da za su fafata takara a babban zabe na 2019.

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya tabbatar da cewa, wakilan jam'iyyar sun daura damara da kulla sulke tare da gwamnoni jam'iyyar wajen rusa wannan kudiri da akida ta shugaban jam'iyyar da kuma Sanatoci masu goyan bayan sa.

Wakilin sun sha alwashin ganin bayan wannan kudiri na zaben 'yar tinke bisa ga goyon bayan akidar gwamnonin jam'iyyar dake da adawa da shugaban jam'iyyar akan wannan lamari.

Zaben fidda gwani: An fara rikici tsakanin Gwamnoni da Shugaban jam'iyyar APC
Zaben fidda gwani: An fara rikici tsakanin Gwamnoni da Shugaban jam'iyyar APC
Asali: Depositphotos

Wani wakilin zaben fidda gwani daga reshen Kudu maso Yammacin kasar nan ya bayyana cewa, ko kadan ba bu adalci cikin wannan lamari na gudanar da zaben 'yar tinke yayin fidda gwanaye na jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Za a dauki Ma'aikata 2000 domin Karantarwa a sabbin Makarantu 40 na jihar Borno

Legit.ng ta fahimci cewa, jihohin da suke goyon bayan wannan lamari na zaben 'yar tinke sun hadar da; Abia, Benuwe, Cross River, Delta, Enugu, Jigawa, Kano, Kwara, Legas da kume Neja.

Sauran jihohin da suka nuna rashin goyon bayan aiwatar da zaben 'yar tinke sun hadar da; Adamawa, Bauchi, Borno, Imo, Kaduna, Katsina, Kogi, Nasarawa, ONdo, Filato, Ribas, Sakkwato, Yobe da kuma Zamfara.

Jihohin da kuma kawowa yanzu ba yanke shawarar akan wannan ra'ayi da akida ba sun hadar da; Ebonyi, Kebbi, Ogun, Oyo, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Gombe, Osun da kuma Taraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel