Ambaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar Kebbi

Ambaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar Kebbi

Kungiyar masu sayar da 'ya'yan itatuwa reshen jihar Kebbi, ta bayyana cewa mambobin ta sun yi asarar dukiya ta kimanin Naira Miliyan 25 sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a babbar kasuwa dake garin Birnin Kebbi.

Shugaban wannan kungiya, Alhaji Aminu Abubakar, shine ya bayyana hakan ga manema labarai cikin Birnin Kebbi a ranar Asabar ta yau da cewar rashin wadatattun magudanan ruwa ya haddasa aukuwar ambaliyar ruwa a babbar Kasuwar.

A sanadiyar haka shugaban kungiyar ke mika kokon barar sa ga gwamnatin jihar akan ta inganta gine-ginen wannan kasuwa domin gudanar da harkokin su cikin annashuwa gai da kwanciyar hankali tare da bunkasar hanyoyin samar da kudaden shiga ga gwamnatin.

Ambaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar Kebbi
Ambaliyar ruwa ta salwantar da 'ya'yan itatuwa na N25m a jihar Kebbi
Asali: Depositphotos

Kazalika shugaban kungiyar ya kuma nemi gwamnatin jihar akan ta agaza da tallafi ga mambobin su da wannan annoba ta ambaliyar ruwa ta afkawa.

KARANTA KUMA: Wani 'Dalibi ya gamu da ajali a Makarantar horas da dakarun Soji, zargi ya fada zuciyar Iyayen sa

Yake cewa wannan tallafi zai taimaka kwarai da aniyya wajen bunkasa harkokin kasuwanci ga 'yan kasuwar ba tare da sun ji wani radadi na asarar da ta afka ma su ba.

Ya kara da cewa, kungiyar ta na da sama a mambobi 20, 000 cikin dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi da suke tallafawa gwamnatin wajen samar da abin yi ga fiye da matasa 3000 masu daukar dako da talla a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel