Sarkin musulmi ya soki gwamnatin shugaba Buhari a kaikaice

Sarkin musulmi ya soki gwamnatin shugaba Buhari a kaikaice

- Sarkin musulmi ya soki gwamnatin shugaba Buhari a kaikaice

- Ya koka kan karuwar yawan kashe-kashe a cikin kasa

- Yayi kira da al'umma su bada hadin kai wajen tabbatuwar zaman lafiya

Sarkin musulmi Mai martaba Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar jiya ya koka da yadda harkoki ke cigaba da dabarbarewa a cikin Najeriya karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari musamman ma yanzu da zabukan shekarar 2019 ke ta kara matsowa.

Sarkin musulmi ya soki gwamnatin shugaba Buhari a kaikaice
Sarkin musulmi ya soki gwamnatin shugaba Buhari a kaikaice
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun gano maboyar 'yan Boko Haram

Sarkin, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi wannan tsokacin ne lokacin da wata tawagar shugabannin addinin kirista suka kai masa ziyara a fadar sa a wani mataki na farko kafin fara babban taron su da suka shirya a garin na Sokoto.

Legit.ng ta tsinkayi cewa Sarkin musulmin ya ce abun takaici ne yadda kashe-kashe ke ta karuwa a cikin kasar nan wasu da sunan addini ko kabilanci.

Haka ma kuma ya ja hankalin 'yan siyasa da cewa bai kamata ba su bari banbancin jam'iyyar ya raba kan su har ma su soma fada a tsakanin su.

Daga karshe ne kuma sai yayi kira ga kowa da kowa da ya mai da hankali wajen ganin tabbatuwar tsaro a kasar baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel