Bidiyo: Atiku Abubakar ya sha ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna

Bidiyo: Atiku Abubakar ya sha ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna

- An yi wa Atiku ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Kaduna

- Fitaccen dan siyasar dai ya gabatar da sallar juma'ar ne a garin na Kaduna

- Yanzu yana neman tikitin takarar shugabancin kasa a PDP

Labarin da muke samu daga majiyar mu ta tabbatar mana da cewa wasu jama'a a garin Kaduna sun yi ta yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna.

Bidiyo: Atiku Abubakar ya sha ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna
Bidiyo: Atiku Abubakar ya sha ihun 'ba ma yi, sai Buhari' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dubun wasu matsafa 13 ta cika a Najeriya

Kamar yadda muka samu, fitaccen dan siyasar dai ya gabatar da sallar juma'ar ne a garin na Kaduna inda bayan an kammala sallar ne jama'a suka fahimci cewa shine kuma suka soma yi masa iyu.

Legit.ng ta samu cewa a baya ne dai Alhaji Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP kafin daga ya nuna sha'awar sa na neman tikitin yin takarar shugabancin kasar a zaben 2019 mai zuwa.

Mai karatu dai in bai manta ba a kwanan baya ma wasu matasan sun yi wa Sanata Kwankwaso 'ihu bama yi' a masallacin Juma'a na Sultan Bello dake Kaduna.

A wani labarin kuma, Wata tsohuwa mai suna Grace Osagie kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu ance wai ta fadi a some a filin jirgin kasa da kasa na jihar Benin inda taje domin tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar.

Kamar dai yadda wani ganau ya shaidawa majiyar mu, yace ana kyautata zaton tsabar zafin rana ne ya sa matar suma biyo bayan cincirindon magoya bayan fitaccen dan siyasar da suka je tarbar sa.

Ga dai bidiyon nan a kasa:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel