Fasinjoji sun shiga zullumi bayan lalacewan jirgin kasa a garin da ake yawan sace mutane

Fasinjoji sun shiga zullumi bayan lalacewan jirgin kasa a garin da ake yawan sace mutane

- Daya daga cikin sabbin jiragen da ke jigilar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja ya lalace a hanya

- Jirgin da lalace ne a kusa da karamar hukumar Jere na jihar Kaduna da ya yi kaurin suna wajen fashi da makami

- Fasinjoji da yawa da ke cikin jirgin sun nuna bacin ransu saboda irin hadarin da aka jefa su ciki na tsayar da su a dokar daji

Wani jirgin kasa mai lamba SP00003 da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya lalace a kan iyakan karamar hukumar Jere da ke jihar Kaduna, garin da ya yi kaurin suna wajen fashi da makami da satan mutane.

Lalacewar jirgin ya saka fargaba da bacin rai a zukatan fasinjojin da ke jirgin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa jirgin ya baro Kaduna ne misalin karfe 10.35 na safiyar Juma'a amma ya tsaya a Jere misalin karfe 12.20 na rana.

Fasinjoji sun kidime yayin da jirgin kasa ya lalace a kauyen da yayi kaurin suna wajen sace mutane
Fasinjoji sun kidime yayin da jirgin kasa ya lalace a kauyen da yayi kaurin suna wajen sace mutane
Asali: Twitter

Jim kadan bayan jirgin ya tsaya, jami'an kula da jirgin sun nemi afuwar fasinjojin inda suka bayyana cewa jirgin ya tsaya ne saboda wata matsala da ta sami injin jirgin sai dai hakan bai kwantar da hankulan wasu fasinjojin ba.

DUBA WANNAN: Dan takarar da ya kamata PDP ta tsayar muddin tana son kada Buhari - Makarfi

Wani fasinja mai suna Usman Bala, ya ce ya yi nadamar shiga jirgin inda ya ce abin takaici ne duk da tsadar kudin jirgin amma ba'a kulawa da jiragen.

"Dama haka Najeriya take. An iya bulo da shirye-shirye masu kyau amma ba'a kulawa da su. Na shiga jirgin ne saboda in hallarci daurin aure misalin karfe 1 na rana amma yanzu na makara.

"Nayi nadamar rashin shiga motar haya. Da yanzu na isa Abuja," inji Usman.

Wata fasinja mai suna Aisha Bature itama ta koka kan yadda wadanda alhakin kulawa da jiragen ya rataya a kansu basu kula da jiragen inda tayi ikirarin suna karkatar da kudaden zuwa wasu abubuwan.

NAN ta ruwaito cewa hukumar da ke kula da jiragen kasa ta turo wani jirgin domin ya karasa da fasinjojin zuwa wuraren da zasu tafi. Mahukuntan kuma sun bawa fasinjojin hakuri inda su kayi alkawarin daukan matakan kare afkuwar irin wannan a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel