Mutane 6 sun shiga hannu bisa laifin lallasa wani Jami'in dan sanda a jihar Osun

Mutane 6 sun shiga hannu bisa laifin lallasa wani Jami'in dan sanda a jihar Osun

Kimanin mutane shida ne suka gurfana a ranar Alhamis ta yau gaban wata kotun majistire dake birnin Osogbo bisa laifin lakadawa wani jami'in dan sanda dukan tsiya, DSP Rowland Adibuah, a yayin da yake bakin aikin sa can jihar Osun.

Wannan Mutane shida da suka aikata wannan babban laifi sun hadar da; Adelu Laide mai shekaru 19, Adebayo Abass dan shekara 18, Babatunde Olamilekan dan shekara 18, Adeleke Qudus dan shekara 19, Asimiu Raji dan shekara 18 da kuma Arowolo Yusuf mai shekaru 20 a duniya.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Sufeto Gafani Musilimi, ya shaidawa kotun cewa wannan Matasa sun aikata laifin ne da misalin karfe 1.30 na ranar Larabar da ta gabata cikin wani filin sallar Idi dake unguwar Tanisi Gbonmi a birnin na Osogbo.

Mutane 6 sun shiga hannu bisa laifin lallasa wani Jami'in dan sanda a jihar Osun

Mutane 6 sun shiga hannu bisa laifin lallasa wani Jami'in dan sanda a jihar Osun
Source: Twitter

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wannan lamari ya auku ne a yayin da DSP Adibuah ke kokarin kwabar wannan Matasa da suke muzgunawa al'ummar yankinsu da shaye-shaye na tabar wiwi.

Matasan cikin zafin kai kuma rike da makamai suka far ma Adebuah inda suka yi ma sa jina-jina tare da targada masa kafafu da a cewar su ya yi yunkurin shigar ma su hanci da kundundune.

KARANTA KUMA: Musulmai sun buƙaci hutun Sabuwar Shekara ta Musulunci

NAIJ.com ta fahimci cewa, laifin wannan Matasa ya sabawa sassa na 355, 356, 73, 213, 516, 70, da kuma sashe na 249 cikin dokokin jihar Osun.

A yayin da Matasan suka roki alfarma ta sassauci da neman afuwa, alkalin kotun, Mista Olatunbosun Oladipo, ya bayar da belin su akan zunzurutun kudi na N200, 000 inda ya kuma daga sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Okotoba domin ci gaba da shari'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel