Garambawul: Sifeta Janar ya haramtawa jami'an FSARS tare motoci da yi masu bincike akan hanya

Garambawul: Sifeta Janar ya haramtawa jami'an FSARS tare motoci da yi masu bincike akan hanya

- A baya NAIJ.com ta ruwaito cewa Mr. Idris, ya sake maimaita gargadin da ya yiwa rundunar FSARS, da su daina muzgunawa jama'a.

- A cikin garambawul da aka yiwa rundunar ta SARS, akwai amincewa da nada kwamishinan yan sanda da zai rinka kula da ayyukan rundunar

- Mr Idris, ya sake haramtawa jami'an SARS tsayar da motoci tare da yin binciken kai tsaye ba tare da wani kwakkwaran izini ba

Sifeta Janar na rundunar yan sanda , Ibrahim Idris, a ranar laraba ya sake maimaita gargadin da ya yiwa runduna ta musamman da ke da alhakin dakile fashi da makami, da su daina muzgunawa jama'a.

A baya NAIJ.com ta ruwaito cewa Mr. Idris, ya yi wannan gargadi ne a wani taron bita da aka shiryawa jami'an hukumar ta SARS a jihar Anambra, a ranar laraba.

"An haramta maku bincike a cikin wayoyi ko na'ura mai kwakwalwa, har sai idan umurnin hakan ya zo kai tsaye daga Sifeta Janar na yan sanda, ko wani babban jami'i da aka bashi ikon bayar da umurnin," a cewar Mr. Idris, tabakin Amaechi Elumelu, kodinetan rundunar X-Squad.

Mr. Elumelu ya kuma gargadi jami'an da su kauracewa ajiye mai laifi na tsawon sama da awanni 48 ba tare da kaishi kotu ba, da cewar duk wani jami'i da aka kama da laifin hakan, to zai fuskanci hukuncin kora.

KARANTA WANNAN: Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

Garambawul: Sifeta Janar ya haramtawa jami'an FSARS tare motoci da yi masu bincike akan hanya

Garambawul: Sifeta Janar ya haramtawa jami'an FSARS tare motoci da yi masu bincike akan hanya
Source: Original

A cikin garambawul da aka yiwa rundunar ta SARS, akwai amincewa da nada kwamishinan yan sanda da zai rinka kula da ayyukan rundunar, wanda sashe ne na rundunar yan sanda da aka samar da ita don magance matsalolin fashi da amakami da garkuwa da mutane.

A makonnin da suka gabata, Mr. Idris ya haramtawa jami'an rundunar bincike kai tsaye ga yan Nigeria, ko bakin da suka shigo daga wasu kasashe. An yi na'am da wannan umurni na Sifeta Janar din, musamman matasan kasar da ke takun saka da jami'an rundunar ta SARS.

Sai dai makonni kadan da bada wannan umurni, yan Nigeria suka fara dari darin sahihancin shugabancin Mr. Idris, inda canje canjen basu wani kankama ba, illa mai karuwar korafe korafe kan yadda jami'an rundunar ta SARS ke gallazawa jama'a

KARANTA WANNAN: Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa

Jin wannan korafe korafe, ya sa Mr. Idris, ya bada cikakkiyar oda, tare da rarraba takardar tsari da dokokin gudanarwa na rundunar. Mr Idris, ya sake haramtawa jami'an SARS tsayar da motoci tare da yin binciken kai tsaye ba tare da wani kwakkwaran izini ba.

A cikin garambawul da akayiwa rundunar ta SARS, an canja mata suna daga SARS zuwa F-SARS, wato ta koma karkashin gwamnatin tarayya. Haka zalika, Mr. Idris ya ce an dage rundunar daga sashen rundunar binciken miyagun laifuka da ta'addanci (FCID) zuwa sashen kaddamar da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
NAIJ.com
Mailfire view pixel