Saukar jirgin Osinbajo a taron kamfen din APC ya saka jama’a farinciki

Saukar jirgin Osinbajo a taron kamfen din APC ya saka jama’a farinciki

Jirgin dake dauke da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sauka a filin taron gagamin kamfen din jam’iyyar APC a birnin Osogbo na jihar Osun. Ana taron yakin neman zaben ne gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar ranar 22 ga wata.

Ana sanar da saukar jirgin Osinbajo da misalign karfe 4:05 na rana sai jama’ar dake wurin taron suka kaure da sowa da farinciki tare da nufar inda jirgin ya sauka.

Saukar jirgin Osinbajo a taron kamfen din APC ya saka jama’a farinciki
Osinbajo a kasuwar Utako kafin ya bar Abuja
Asali: Twitter

Manyan ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka halarci taron sun yi tururwa domin gaisawa da mataimakin shugaban kasar. Daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da suka kewaye Osinbajo domin gaisawa da shi bayan ya sauka, akwai gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun, shugabn masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel