Na bar N13bn a asusun ajiya na Gwamnatin Jihar Sakkwato - Bafarawa

Na bar N13bn a asusun ajiya na Gwamnatin Jihar Sakkwato - Bafarawa

Daya daga cikin jiga-jigan 'yan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa sai da ya bar zunzurutun dukiya har ta N13bn cikin asusun gwamnatin jihar Sakkwato a yayin saukar sa daga kan kujerar gwamnan jihar.

Bafarawa ya bayyana hakan ne cikin birnin Owerri yayin da ya ziyarci masu ruwa da tsaki a skelkwatar jam'iyyar PDP ta jihar Imo, domin neman goyan bayan su kan kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, a yayin da shafe tsawon shekaru takwas kan kujerar gwamnatin jihar Sakkwato, ko sau guda bai karbi albashinsa ba inda ya rika sadaukar da wannan kudade wajen ci gaba da kuma bunkasar jihar.

Na bar N13bn a asusun ajiya na Gwamnatin Jihar Sakkwato - Bafarawa
Na bar N13bn a asusun ajiya na Gwamnatin Jihar Sakkwato - Bafarawa
Asali: Depositphotos

'Dan takarar kujerar ta shugaban kasa ya kuma bayyana cewa, nasara gami da wanke kansa daga zargin da hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC ta yi ma sa a baya ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kasanacewa tsarkakakken dan siyasa a kasar nan.

KARANTA KUMA: An cafke wasu Soji da aka sallama dumu-dumu cikin aikata miyagun laifi

Ya kara da cewa, yana ci gaba da jajircewa da hankoron kujerar shugaban kasa sakamakon muradi gami da burin zuciyar sa na bunkasa da habakar tattalin arziki domin alfanun dukkanin al'ummar kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Bafarawa na ci gaba da karade yankin Kudu maso Gabashin kasar nan domin neman bayan al'ummar jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da kuma Imo kan kudirin sa na takarar kujerar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel