Atiku Abubakar ya fadi manyan matsalolin shugaba Buhari

Atiku Abubakar ya fadi manyan matsalolin shugaba Buhari

- Atiku Abubakar ya fadi manyan matsalolin shugaba Buhari

- Yace Buhari bai jin shawara sannan ya cika taurin kai

- Ya nuna shakku game da sahihancin zaben da za'a yi a 2019

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wasu halaye da yake zargin shugaba Muhammadu Buhari yana da su da ka iya kawo barazana ga sahihancin zabukan 2019.

Atiku Abubakar ya fadi manyan matsalolin shugaba Buhari
Atiku Abubakar ya fadi manyan matsalolin shugaba Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya cika wani alkawarin sa ga 'yan Najeriya

Majiyar mu ta tsinkayi fitaccen dan siyasar yana cewa "Shugaba Buhari wanda tsohon soja ne yana da kafiya da rashin jin shawara sannan kuma gashi yana da bala'in son mulki.

"Wadannan da ma wasu halayen sa ne yasa nike da shakku matuka game da yiwuwar samun sahihin zabe a karkashin kulawar sa.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Atiku Abubakar ya kara da cewa sabanin tsohon shugaba Jonathan wanda kowa ya shaide shi ba mai son rigima bane da tashin hankali, shi Buhari sam ba haka yake ba.

Daga karshe ya kuma ja hankalin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta tabbatar da yin adalci ga kowa.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace shi tun da Allaha yayi shi bai taba satar ko da kwandala ba.

Fitaccen dan siyasar haka zalika ya kalubalanci duk wani mai shaidar cewa ya taba karkatar da dukiyar al'umma ko kuma wata rashawa ko cin hanci da ya fito ya fallasa hakan a idon duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel