2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari

2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari

Kasa da makonni uku kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC ), mambobin jam’iyyar babin jihar Sokoto sun tsayar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takaran da suke so ya samu tikitin jam’iyyar.

Haka zalika, jam’iyyar ta nuna amincewarta ga shugaban kungiyar sanatocin arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sannan sun bayyana shi a matsayin shugaba guda a jihar.

Wannan hukunci na daga cikin matsayar da suka tsaya kai a karshen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Sokoto a ranar Talata, 5 ga watan Satumba wadda ya samu halartan shugabannin jam’iyyar a jihar, da masu ruwa da tsaki jam’iyyar.

2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari
2019: APC Sokoto sun tsayar da Shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ne ya jagoranci ganawar wadda aka gudanar cikin sirri, inda ya bayyana Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin uban jam’iyya nagari aa jihar.

KU KARANTA KUMA: Rashin tabbass a Kano yayinda tsohon gwamna Shekarau ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan ta tace za’a samar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct” kenan a turance.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel