Kudaden Shiga: Hukumar Kastam ta samar da N140bn a watan Agusta

Kudaden Shiga: Hukumar Kastam ta samar da N140bn a watan Agusta

Mun samu cewa hukumar kastam ta Najeriya ta yi wata gagarumar bajinta da ba ta taba makamanciyar ta ba cikin wata guda a tarihin Najeriya a yayin da ta ke ci gaba da jajircewa wajen samar da kudaden shiga a kasar nan.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta bayyana a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana cewa, ta samar da zunzurutun kudi na N140.4bn na kudaden shiga da tara cikin watan Agusta kadai na wannan shekara ta 2018.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, shugaban hukumar, Kanal Hameed Ali, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai da cewa, hukumar ta yi wannan gagarumar bajinta a sakamakon sabbin tsare-tsare da gindaya na dakile tsiyayar kudaden shiga a dukkan tashoshin ta.

Kudaden Shiga: Hukumar Kastam ta samar da N140bn a watan Agusta
Kudaden Shiga: Hukumar Kastam ta samar da N140bn a watan Agusta
Asali: Depositphotos

Kazalika hukumar ta shimfida tsare-tsare tare da hadin gwiwar yarjejeniya da masu ruwa da tsaki wajen inganta harkokin ta na gudanarwa da kuma abokanan huldar ta.

Sanarwar da kakakin hukumar ya bayyana, Joseph Attah yake cew,a hukumar ta taki wannan babbar nasara a sakamakon wasu muhimman tsare-tsare da ta shimfida wajen tanadar kudaden shiga a matsayin wani jigo na bunkasa tattalin arziki a kasar nan.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya ƙulla tuggun garkuwa da kisan Mahaifin sa a jihar Osun

Legit.ng ta fahimci cewa, a sakamakon wannan tsayuwar daka ta hukumar gami da jajircewa ya sanya ta samar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 140 cikin watan Agusta kadai.

A yayin haka hukumar ta kuma yi kira ga al'ummar kasar nan akan taimakon rahotanni dangane da duk wani lamari da zai tallafa wajen daile faskauri da bunkasar tattalin arziki da ciyar da kasar nan gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel