Birkice gidan Clark: An kama dan tsurkun da ya yiwa 'yan sanda ingiza mai kantu

Birkice gidan Clark: An kama dan tsurkun da ya yiwa 'yan sanda ingiza mai kantu

- An kama mutumin da ya tsegunta wa 'yan sanda cewa akwai makamai a gidan Edwin Clark

- Mutumin mai suna, Ismail Yakubu, ya bayyana yada ya samo bayyanin

- 'Yan sanda sunce za'a gurfanar da Yakubu a kotu domin ya fuskanci hukunci

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kama wani Ismail Yakubu da ake zargi da bayar da bayannan karya da ya janyo jami'an yan sanda suka kai sumame gidan Cif Edwin Clark a ranar Talata.

Yakubu mazaunin wani kauye ne mai suna Waru da ke Apo a babban birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar yan sanda, Jimoh Moshood, ya ce za'a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu a yau Laraba bisa tuhumarsa da laifin yiwa 'yan sanda karya.

Ya kuma kara da cewa jami'an 'yan sanda hudu da su kayi sumamen suna tsare har zuwa lokacin da za'a kammala bincike da Sufeta Janar na 'yan sanda ya bayar da umurnin da gudanar.

Birkice gidan Clark: An kama dan tsurkun da ya yiwa 'yan sanda ingiza mai kantu
Birkice gidan Clark: An kama dan tsurkun da ya yiwa 'yan sanda ingiza mai kantu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa za'a ladabtar da jami'an yan sandan bayan an kammala binciken.

DUBA WANNAN: Gyaran jadawalin zabe: PDP ta bukaci majalisa ta saka takalmin karfe ta take Buhari

Da yayin da yake amsa tambayoyin 'yan sanda, wanda ake zargin ya ce ya shiga motar haya ne zuwa Asokoro domin ziyarar abokinsa sai suka lura cewa an kule titin zuwa gidan Edwin Clark wai sai direban motar ya fada masa cewa ya ga wata mota kirar hilux dauke da makamai ta shiga gidan.

"An kule titin, babu hanyar shiga ko fita. Saboda haka sai nayi tambaya sai direban da ya dauko ni ya ce mutanen Neja-Delta ke zama a unguwar. Sai ya nuna wata farar mota da ke shiga gidan. Na duba sai naga gidan na da lamba 43. Direban ya ce min motar cike ta ke da bindigogi." inji Yakubu.

Moshood ya kara da cewa jami'an 'yan sanda da su kayi bincike a gidan basu bi doka ba saboda ya kamata su nemo izinin shiga gidan amma ba haka su kayi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel