Shugaban Yansanda mai murabus ya kakkabe rigarsa ya shiga takarar Sanata a Jigawa

Shugaban Yansanda mai murabus ya kakkabe rigarsa ya shiga takarar Sanata a Jigawa

Tsohon shugaban rundunar Yansandan Najeriya a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sulaiman Abba ya fada cikin rububin takarar neman kujerar Sanata a jahar Jigawa, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abba na takarar mukamin Sanata mai wakiltar mazabar Jigawa ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, wanda a yanzu haka wani tsohon babban jami’in hukumar kwastam, Sabo Nakudu yayi dare dare akai.

KU KARANTA:

Shugaban Yansanda mai murabus ya kakkabe rigarsa ya shiga takarar Sanata a Jigawa
Sulaiman
Asali: Depositphotos

A wata hira da aka yi da Abba, ya bayyana cewa rundunar yansandan Najeriya a karkashinsa ne ta tilasta ma tsohon shugaban kasa Jonathan amincewa da shankaye a zaben shekarar 2015 wanda shugaba Buhari ya samu galaba akansa.

“Alhamdulillahi, mu muka tilasta ma wadanda suka fadi zabe yarda da shan kayen da suka yi, duk kokarin da aka na ganin mun kawo cikas ga zaben bayan an bayyana sakamakonsa an yi, amma duk da haka muka nuna tirjiya.” Inji shi.

Shi dai Sulaiman Abba wanda Jonathan ya tsigeshi daga mukaminsa na babban sufetan Yansanda jim kadan bayan kammala zaben shekarar 2015 dan asalin jahar Jigawa ne, kuma yana da digiri a fannin tarhi daga jami’ar Jos da kuma digiri a fannin shari’a daga jami’ar Abuja.

Sulaiman Abba ya yi kwamishinan Yansanda a jihohin Legas da Ribas, haka zalika ya rike mukamin jami’in Dansanda mai kula da shiyya ta bakwai daga nan ya samu karin girma zuwa babban sufetan Yansanda.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel