Najeriya ce kasa ta 43 a cikin kasashen Duniya da suka fi karfin Soja

Najeriya ce kasa ta 43 a cikin kasashen Duniya da suka fi karfin Soja

A lokacin da kake raina naka, a wannan lokacin ne kuma wani ke ganin girman nakan, kamar yadda wata cibyar bincike akan al’amuran tsaro na Duniya ta tabbatar game da karfin Sojojin Najeriya.

Cibiyar ‘Global Fire Power’ ce ta gudanar da wannan bincike a shekarar 2018, inda ta daura Najeriya a mukamin kasa ta arba’in da uku (43) a cikin jerin kasashen Duniya dake da suka fi karfin Soja, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Ladan noma: Wani manomi ya dauki alwashin sayan ma Buhari takardar takara

Najeriya ce kasa ta 43 a cikin kasashen Duniya da suka fi karfin Soja
Sojoji
Asali: Facebook

Sai dai cibiyar ta bayyan Najeriya a matsayin ta hudu a karfin Soja a nahiyar Afirka, a bayan kasar Misra, Aljeriya da kasar Afirka ta Kudu, inda tace Najeriya nada dakarun Soja dubu dari da tamanin da daya (181,000), daga cikinsu Sojoji dubu dari da ashirin da hudu suna aiki, yayin da dubu hamsin da bakwai ke jiran kota kwana.

Wasu daga cikin manyan kasashen nahiyar Turai da Najeriya ta fisu karfin Soja sun hada da Denmark, Belgium, Portugal, Bulgaria, Austria, Ireland, Macedonia, Finland, Hungary, Croatia, Slovakia, Serbia, Albania, Lithuania, Latvia, Estonia, Slovenia, Bosnia da Herzegovina.

Najeriya ce kasa ta 43 a cikin kasashen Duniya da suka fi karfin Soja
Sojoji
Asali: Facebook

Amma fa wannan bincike ya tabbatar da kasar Amurka a matsayin kasar da tafi kowacce kasa karfin Soja a Duniya, inda ta buge kasashen Rasha da China. Amurka na da Sojoji miliyan biyu da dubu dari takwas da talatin da dari daya (2, 830, 100).

Daga karshe rahoton binciken yace Amurka nada jiragen yaki dubu goma sha uku da dari uku da sittin da biyu (13, 362), jiragen daukan motocin yaki ashirin (20) da motocin yaki guda dubu talatin da tamanin da takwas (38, 888), Igwa Igwa dubu biyar da tamanin da takwas (5, 888) da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel