Fitaccen musulmin dan kwallon Duniya ya wanke bandakin masallaci a Ingila

Fitaccen musulmin dan kwallon Duniya ya wanke bandakin masallaci a Ingila

Watau idan aka ga yadda wasu mutanen da Allah ya daukaka kuma ya azurtasu suna kaskantar da kansu a kasashen Duniya, sai abin ya baiwa jama’a mamaki, musamman idan tawali’un ya danganci maslahar addinin Musulunci ne.

Jaridar ‘Evening Standar’ ta kasar Birtaniya ta ruwaito shahararren musulmin dan wasan kwallon kaga dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Sadio Mane ya sanya hannu cikin aikin gayya wajen wanke bandakin wani masallaci.

KU KARANTA: Najeriya, UN da wasu manyan kasashe 2 zasu lalubo hanyar kawo karshen Boko Haram a Turai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mane yayi wannan aikin alheri ne jim kadan bayan wasan Liverpool da Licester, inda ya zura kwallo daya suka ci Leicestr 2-1, sakamakon a wannan Masallaci yake sallah, masallacin Al-Rahma dake titin Mulgrave a birnin Liverpool.

An haifi Mane ne a cikin addinin Musulunci, kuma ya girma a garin Bambali dake kudancin kasar Sengal inda mahaifinsa ne limamin Masallacin garin, hakan ya sanya shi mutumi mai riko da addini.

A wata hira da yayi, Mane ya bayyana cewa “Bana shan giya saboda addinina na da matukar muhimmanci a gareni, ina bin dokokin addinin Islama, kuma ina salloli na biyar a kowacce rana, bana fashi.

“Kasar Senagal kasace mai dauke da kasha 90 Musulmai, kasha 10 Kiristoci, kuma muna zaman lafiya da juna ba tare da wata matsala ba, hatta babban abokina Luke kirista ne, kuma yana zuwa gidanmu, nima ina zuwa gidansu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel