2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa

2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa

- Alamu sun nuna Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara zai samu babban abokin adawa dake hararan kujerarsa

- Gashion Daniel Danna, ya kaddamar da ra’ayinsa na takarar kujerar majalisar wakilai

- Danna yace Dogara ya shafe zango uku akan kujerar don haka ya kamata a basu dama suma

Wani dan majalisa a Bauchi, Gashion Daniel Danna, ya kaddamar da ra’ayinsa na takarar kujerar majalisar wakilai na mazabar Tafawa Balewa da Bogoro a majalisar dokokin kasa a zabe mai zuwa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda zai kara da Yakubu Dogar, kakakin majalisar wakilai.

Da yake Magana da manema labarai a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba, jim kadan bayan ya gabatar da fam dinsa a sakatariyar PDP dake Bauchi, lauyan mai shekaru 37 ya bayyana cewa Dogara, dan asalin yankin, ya dade akan kujerar kusan zango uku kenan, inda ya kara da cewa domin adalci, ya kamata a bar karamar hukumar Tafawa Balewa ta samar da wani dan takara a zabe mai zuwa.

2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa
2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa
Asali: Depositphotos

Danna yace: “Ya kamata a ba matasa damar rike mukaman siyasa a 2019 domin sune suka shafe kaso 60 cikin dari na kasar. Na yanke wannan muhimmin shawara ne saboda tarin goyon bayan da na samu daga mazabana.

“Tsawon shekau biyu da suka gabata, ina ziyartan mazaban sannan na hade da mazabana domin haduwa da duk masu fada a ji. Na shiga takaran ne saboda yawan kira da na samu daga mutane na, inda suka nemi nayi takarar kujerar saboda kwazona, da kuma karfin aiki.

“Na san cewa zan iya wakiltansu sosai. Shugaban PDP a jihar Alhaji Hamza Akuyam, wadda ya samu wakilcin mataimakin shugaban jamiyyar na jihar Alhaji Haruna Musa Shitu yayi alkawarin yin adalci ga dukkanin yan takara, inda ya gargade su da sauya sheka zuwa sauran jam’iyyun siyasa idan suk gaza cin zaben fidda gwani.”

KU KARANTA KUMA: 2019: Yan takaran PDP a Kogi sun hana a ba Melaye da sauransu tikitin tazarce

A halin da ake ciki, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Uche Secondus yayi zargin cewa barayin yan siyasa na hada runduna domin dawo da Shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Da yake Magana yayin kaddamar da kungiyar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun da za’a gabatar a ranar 22 ga watan Satumba, Secondus yace jam’iyyar APC ta mayar da kanta mafakar barayi inda ya kara da cewa irin wadannan mutanen na samun kariya da kwanciyar hankali.

Shugaban PDP din yace rashawa mafi muni shine magudin zabe da siyan kuri’u .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel