Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa

Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa

Mun samu cewa hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta yi wata gagarumar nasara ta cafke wasu miyagun 'yan ta'adda da suka shahara da kashe-kashe, garkuwa da mutane, kwacen motoci gami da fashi da makami a wasu birane da kauyukan Arewa.

Hukumar ta samu nasarar cafke 'yan ta'addan 31 da suka sharaha da addabar al'umma a kauyuka da biranen Abuja, Kaduna, Birnin Gwari, Funtua da kuma jihar Zamfara.

A garin Tafa dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, DCP Jimoh Moshood, ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, inda ya ce 'yan ta'adda 31 sun shiga hannu tare da muggan makamakan su na ta'addanci.

Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa
Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa
Asali: Depositphotos

Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa
Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa
Asali: Facebook

Yake cewa, a sakamakon tsayuwar daka kan samar da tsaro ta sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim k. Idris, ya sanya hukumar ta dukufa wajen kawo karshen ta'addanci gami da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali musamman ga matafiya dake ketare wannan yankuna a yayin sufuri.

Kazalika sufeton ya tsanantawa jami'an sa akan kawo sabbin tsare-tsare da zasu kawo karshen kisan gillar al'umma musamman a jihohin Kaduna, Neja, Zamfara, Kogi, Benuwe da kuma wasu sassa na jihar Filato.

KARANTA KUMA: Rayuka 14 sun salwanta yayin da Makiyaya suka kai hari jihar Filato

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar cafke 'yan ta'adda 31 da suka hadar da kwamandun 'yan baranda dake zubar da jinin al'umma a jihar Zamfara da kuma wadanda suke yi garkuwa da babban Malamin nan Sheikh Muhammad Ahmed Alqarkawi inda suka bayar da fansar sa akan Naira miliyan 12.

DCP Moshood ya kara da cewa, hukumar nan ba da jimawa ba za ta bayyana sunayen wannan 'yan ta'adda domin ya zamto izina ga sauran al'ummar kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel