Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayar da shawarar yiwa barayin gwamnati afuwa idan ana son cin ribar yaki da rashawa

- Ya ce yi musu afuwa sai sanya su dawo da wani kaso mai tsoka cikin kudin ko kuma su dawo dashi su sany jari a Najeriya

- A cewarsa, akwai kudade masu yawa a asusun kasahen waje da makabarta da gidajen karkashin kasa da gara ke cinyewa

Gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya David Umahi ya bayyana cewa mafi yawa daga cikin wadanda suka sace kudaden gwamnati suna boye kudaden ne a bankunan kasashen waje, makabarta da gidajen karkashin kasa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a jiya Litinin a wajen taron kaddamar da shirin bayar da horo kan yaki da rashawa da koyar da da'a da aka shirya wa ma'aikatun kananan hukumomin jihar a birnin Abakaliki.

Barayin gwamnati na boye kudade a makabarta - Wani gwamnan PDP
Barayin gwamnati na boye kudade a makabarta - Wani gwamnan PDP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: PDP za tayi amfani da kai ne ta jefar - Tsohon gwamnan jam'iyyar

Gwamnan kuma ya bayar da shawarar cewa ya dace a rika yiwa barayin gwamnati afuwa saboda hakan zai sanya su mika kansu ga hukuma kuma su dawo da 70% na kudaden jama'a da suka sace.

Kazalika, gwamnan ya yi alkawarin gina ofishin hukumar yaki da rashawa ICPC a jiharsa saboda taimakawa wajen yaki da rashawa.

"Akwai dimbin kudaden da barayin gwamnati suka sace a asusun ajiya a bankunan kasashen waje da makabartu da gidajen karkashin kasa da ake birne gara na cinyewa.

"Amma idan da za'ayi yarjejeniya da wadanda suka aikata laifin ta yadda zasu dawo da 70% ko kuma a bukaci su dawo da kudaden su saka jari da su a Najeriya, hakan zai sa mu karbo kudade da yawa kuma muyi amfani dashi wajen gina kasa," inji Umahi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel