APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

- Jam'iyya mai mulki ta APC ta bayyana dalilinta na bin tsarin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

- Shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole ya ce sabon tsarin zai magance matsalolin da ke tattare da yin zabe ta hanyar jami'ai

- Adams Oshiomhole, ya ce akwai yiyuwar jam'iyyar ta sake fasalin sabon tsari, domin gudanar da shi a dukkanin matakai na shugabanci

A shirin da take yi na fuskantar babban zaben 2019, shugaban jam'iyya mai mulki ta APC na kasa, Adams Oshiomhole a jiya litin, ya ce jam'iyyar ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani, don bunkasa siyasar cikin gida.

Ya shaidawa jaridar The Nation cewa jam'iyyar ta zabi mayar da dukkanin mambobinta zama jami'an da zasu kada kuri'a a zaben fitar da yan takara a matakai daban daban.

Ya ce wannan sabon tsarin zai magance matsalolin da ke tattare da tsarin zabe ta hanyar wasu tsirarun jami'ai (delegates), da suka hada da cin hanci, wanda ke haddasa rikicin cikin gida a duk lokacin da aka kammala zaben.

Sai dai Oshiomhole ya bayyana cewa, akwai matsaloli da ke tattare da zaben fitar da gwani ta hanyar yin kato bayan kato, da suka hada da matsalolin tsaro, wanda ya ce a yanzu ake kan nazarin samar da hanyoyin magance su.

KARANTA WANNAN: Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani
APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani
Asali: UGC

Da ya ke kare tsarin kato bayan kato, ya ce: "Mambobin jam'iyyar sun dade suna korafi na zama saniyar ware a zaben fitar da gwani na jam'iyyar, sai dai fa idan anzo zaben gama gari ne ake damawa da su. Su kuma suna so a fara damawa da su tun a matakin farko.

"Haka zalika mun fahimci cewa tsarin kato bayan kato ba ya tattare da matsalolin da ke cikin tsarin zabe ta hanyar jami'ai. Ba zaka iya yin murdiya a tsarin kato bayan kato ba, haka kuma ba zaka iya cin zabe ta hanyar bayar da cin hanci ba.

"Muna son bunkasa demokaradiyya. Muna son baiwa dukkanin mambobi damar nuna karfin ikonsu akan jam'iyyar."

A cewar shugaban jam'iyyar, mafi akasarin masu adawa da tsarin kato bayan kato gwamnoni ne, wadanda za su ci karen su ba babbaka idan har aka ce za'ayi tsarin zabe ta hanyar jami'ai.

Ya ce: "Gwamnoni da ke da iko kan kwamishinoni, masu basu shawara, manyan masu tallafa masu, shuwagabannin kananan hukumomi, na ci gaba da nuna tsoronsu na gudanar da zaben fitar da gwani ta hanyar kato bayan kato. Amma sanatoci sun amince da hakan dari bisa dari, saboda mafi akasarinsu na da matsala da gwamnonin jiharsu.

"Idan aka ce a yi zabe ta hanyar jami'ai, sanatocin ba zasu kai labari ba saboda rikicinsu da gwamnoninsu, amma idan aka yi zaben kato bayan kato, da yawansu na da yakinin samun nasara."

Sai dai, shugaban jam'iyyar ya ce a yayin da aka zabi yin kato bayan kato a zaben shugaban kasa kawai, akwai yiyuwar jam'iyyar ta sake fasalin tsarin, don ayi hakan a dukkanin matakai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel