Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku

Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Aiku Abubakar a jiya Lahadi, 2 ga watan Satumba ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tuhume shi akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar a lokcin da yake kan kujerar mulki.

Atiku wanda ke kan gaba wajen takarar kujerar shugabancin kasa a zaben 2019, ya bayyana cewa tuhumar shine horon da ya sha kan goyon sake fasalin lamuran kasar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar Yarbawa na Afenifere karkashin jagoranci Cif Ayo Adebanjo suka karbi bakuncinsa.

Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku

Sai da Obasanjo ya tuhume ni akan goyon bayan sake fasalin lamuran kasar - Atiku
Source: Depositphotos

Atiku ya bayyana cewa jajircewarsa akan sake fasalin lamuran kasar ya kasance gaskiya kuma wannan ya taba sanya shi wajen fuskantar tuhuma a matsayin mataimakin shugaban kasa.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa kungiyar nan ta Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa za ta marawa Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar baya a zaben 2019. Shugaban Kungiyar Ayo Adebanjo ya fadi haka wajen wani taro da aka yi a makon jiya.

KU KARANTA KUMA: Babu wani tantancewa da za’a yiwa Saraki, Atiku, Kwankwaso da sauransu a yanzu

Kamar yadda labari ya zo mana, Kungiyar Afenifere za ta goyi bayan Atiku Abubakar ne saboda aniyar sa na yi wa tsarin kasar nan garambawul.

Kungiyar tace ba tun yau Atiku ya fara yin wannan kira na sauyawa Najeriya fasali ba. Adebanjo yace fiye da shekaru 10 da su ka wuce kenan Atiku yana fafatuka wajen ganin an yi wa tsarin Najeriya garambawul domin cigaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi

Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel