Yan bindiga sun farfado a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane biyu

Yan bindiga sun farfado a hanyar Kaduna-Abuja, sun kashe mutane biyu

Ana murna sun tafi, ashe da sauran rina a kaba, wannan shine halin da yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka jefa al’ummomin dake rayuwa a yankin hanya Kaduna zuwa Abuja, da ma matafiya dake bin hanyar akai akai.

Ayyukan masu garkuwa da yan bindiga sun sake farfadowa akan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda a ranar Lahadi, 2 ga watan Satumba suka bude ma wata kota dauke da fasinjoji wuta, inda suka kashe mutum biyu, suka yi awon gaba da wasu da dama, inji rahoto jaridar daily Nigerian.

KU KARANTA: PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani daga cikin direbobin daya gamu da wannan bala’a Abubakar Barau yana cewa “Ina tafiya akan hanyar Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 5 na yamma sai na hangi mutane uku a tsakiyar hanya, ba tare da dakatar damu ba kawai suka suka bude mana wuta.

“Ganin haka yasa na yanke shawarar bi ta kan daya daga cikinsu, amma sai suka koma gefen hanya, suka cigaba da yi mana ruwan wuta, ni kuma na cigaba da gud har muka tsere musu, saboda idanma na tsaya kashe mu zasu yi, a haka muka tsira, amma fa motarmu ta sha ruwan harsasai.” Inji shi.

Barau ya cigaba da fadin “Da muka isa garin Kateri, sai muka tarar da Yansanda, inda na tsaya na bayyana musu abinda ya faru, sa’annan na tabbatar musu yan bindigan suna nan suna tare mutane, amma sai Yansandan suka ce ba zasu iya tinkararsu ba, anan dai muka canza taya muka cigaba da tafiya.”

Barau yace har ya gama canza tayar motarsa babu wata mota data fito ta wuce, wannan shine alamar yan bindigan sun tare mutane da dama kenan, daga bisani ya ta tabbatar da an kashe mutane biyu, an yi garkuwa da wasu da dama.

Shima Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da kashe mutane biyu da yan bindigan suka yi, sai dai yace ba tare da bata lokaci ba suka aika Yansanda wajen inda suka yi batakashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel